Labarin Tanko Da Matarsa… Wata rana ne, bayan Tanko ya yi - TopicsExpress



          

Labarin Tanko Da Matarsa… Wata rana ne, bayan Tanko ya yi Sallar magariba ya komo gidansa, sai matarsa ta ce da shi don Allah zo ka ga wani abu, suna fitowa tsakar gida da yake lokacin daidai da lokacin watan musulunci ya raba ne, ya fito ya yi fari tas, sai ta ce da shi ka ga watan nan? Ya ce da ita na ganshi mana, ta ce wallahi ganin fuskarka nake yi ta fi shi fari da kuma haske, ya yi murmushi ya ce da ita, to ke bin fa, ai kema taki fuskar ta fi hasken watan a wajena. Wannan lamari yasa da ya fito ya habu da abokinsa, sai ya ke bashi labarin faranta masa rai da matar tasa ta yi. Bayan ya gama bai wa abokin nasa labarin, take abokin ya tafi gidansa, yana shiga cikin gidan ya kira matarsa ya ce da ita, wance zo ki ga wani abu tana fitowa ya ce da ita kin ga wannan watan? Ta ce da shi, ni makauniya ce? Ya ce da ita don Allah da shi da fuskata wanne ne ya fi haske? Sai ta ce da shi amma wallahi ba ka da hankali. Sai kawai ta yi gaba abinta ta bar shi da tagumi
Posted on: Sat, 21 Sep 2013 01:51:17 +0000

Trending Topics




© 2015