Labarin Wasanni TSAYUWAR KOWACE KUNGIYA A TEBURIN GASAR ZAKARUN - TopicsExpress



          

Labarin Wasanni TSAYUWAR KOWACE KUNGIYA A TEBURIN GASAR ZAKARUN TURAI {CHAMPIONS LEAGUE} KUNGIYOYIN DA SUKA TSALLAKE ZUWA ZAGAYE NA GABA DA KUMA YAN WASAN DA SUKA FI ZURA KWALLO- Sharhi Na Musamman Da yake saura ragowar wasa daya a gama wasannin rukuni na gasar zakarun turai, Chelsea, Mancheter United da Manchester City na daga cikin kungiyoyi 8 da suka tsallake zuwa zagaye na gaba. Real Madrid, Barcelona, Bayern Munich, Paris St. Germain da Atletico Madrid ma sun tsallake. Arsenal- duk da cewa ta lashe wasanni 4 cikin 5 na rukunin F na daga cikin kungiyoyin dake fatan ganin ta samu gurbi cikin gurabe 8 da suka rage. RUKUNIN A 1. Manchester United (11) 2. Shakhtar Donetsk (8) 3. Bayer Leverkusen (7) 4. Real Sociedad (1) ¤ Manchester United sun tsallake zuwa zagaye na gaba, amma basu da tabbacin karewa a matsayi na 1. Idan Manchester United ta samu nasara ko tayi kunnen doki da Shakhtar a wasan su na gaba, za ta kare a matsayi na 1, inda zaa samu na 2 tsakanin Shakhtar din da Bayer Leverkusen. Leverkusen na bukatar doke Real Sociedad a Spain kuma tayi fatan kada Shakhatar ta doke Manchester United a Old Trafford. Idan Shakhtar ta ci United, za ta hau matsayi na 1. Tsakanin Shakhtar da Bayer Leverkusen daya zai kare a matsayi na 3 kuma ya tafi Europa. RUKUNIN B 1. Real Madrid (13) 2. Juventus (6) 3. Galatasaray (4) 4. Kobenhavn (4) ¤ Real Madrid ta kare a matsayi na 1 kuma ba zaa iya kamota ba. Idan Juventus ta samu nasara ko tayi kunnen doki da Galatasaray za ta kare a matsayi na 2. Galatasaray ma za ta tsallake zuwa zagaye na gaba idan ta ci Juventus. Kobenhavn za ta iya karewa a matsayi na 3 idan tayi kunnen doki ko taci Real Madrid, sannan Juventus taci Galatasaray. RUKUNIN C 1. Paris Saint-Germain (13) 2. Olympiakos (7) 3. Benfica (7) 4. Anderlecht (1) ¤ Paris Saint- Germain ta kare a matsayi na 1 kuma baa samu nasara a kanta ba. Olympiakos za ta tsallake zuwa zagaye na gaba idan ta samu nasara akan Anderlecht, amma idan ta kasa yin nasara kuma Benfica ta ci PSG, to Benfica ce za ta tsallake. Anderlecht a ta kare a matsayi na karshe. RUKUNIN D 1. Bayern Munich (15) 2. Manchester City (12) 3. CSKA Moscow (3) 4. Victoria Plzen (0) ¤ Bayern Munich da Manchester City sun tsallake zuwa zagaye na gaba. Manchester City ka iya karewa a matsayi na 1 idan ta doke Bayern Muncih da ci 3-0. Victoria Plzen ka iya karewa a matsayi na 3 idan ta ci CSKA Moscow da ci 2-0. RUKUNIN E 1. Chelsea (9) 2. Basel (8) 3. Schalke (7) 4. S. Bucharest (3) ¤ Chelsea ta tsallake zuwa zagaye na gaba, amma ba za ta kasance a na 1 ba har sai ta doke S.Bucharest a ragowar wasansu. Basel za tabi bayan Chelsea a matsayi na 2 idan Schlake bata samu nasara akanta ba. RUKUNIN F 1. Arsenal (12) 2. Borussia Dortmund (9) 3. Napoli (9) 4. Marseille (0) ¤ Arsenal za ta tsallake zuwa zagaye na gaba idan har baa zura mata kwallayen na suka wuce 2 ba. Dortmund za ta tsallake idan ta samu nasara a wasanta da Marseille. Napoli na bukatar zurawa Arsenal kwallaye 3-0 domin samun damar tsallakewa. RUKUNIN G 1. Atletico Madrid (13) 2. Zenit St. Petersburg (6) 3. FC Porto (5) 4. Austria Wien (1) ¤ Atletico Madrid ta kare a matsayi na 1. FC Porto ka iya tsallakewa idan ta samu nasara akan Atletico Madrid sannan tayi Austria Wien ta doke Zenit. Zenit ka iya tsallakewa a matsayi na 2 idan ta samu nasara akan Austria Wien RUKUNIN H 1. Barcelona (10) 2. AC Milan (8) 3. Ajax (7) 4. Celtic (3) ¤ Barcelona ta tsallake zuwa zagaye na gaba, amma tana bukatar doke Celtic a wasanta na gaba don samun damar karewa a matsayi na 1. AC Milan ka iya karewa a matsayi na 1 idan ta samu nasara akan Ajax sannan kuma Celtic ta doke Barcelona. Ajax na bukatar doke AC milan a Sansiro don samun damar tsallakewa. YAN WASAN DA SUKA FI ZURA KWALLO 1. Cristiano Ronaldo (8) 2. Zlatan Ibrahimovic (8) 3. Lionel Messi (6) 4. Sergio Aguero (6) Admin:- Jamilu Hashimu JH
Posted on: Thu, 28 Nov 2013 20:31:17 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015