MATSALAR SHARA DA BOLA A GEFEN MANYAN TITUNAN GARIN BAUCHI, BABBAN - TopicsExpress



          

MATSALAR SHARA DA BOLA A GEFEN MANYAN TITUNAN GARIN BAUCHI, BABBAN BIRNIN JIHAR BAUCHI BIsmillahir Rahmanir Raheem. Wasallahu Alan Nabiyyil Kareem, waalaa Aalihi, wasahabihi ajmaeen. Zan fara wannan bayani nawa, akan matsalar shara da bola da suke neman mamaye manyan titunan cikin garin Bauchi, da wadansu baitoci guda biyu na Marigayi Mallam Saadu Zungur, Allah Ya rahamsheshi, Ya kuma gafarta masa. A wadannan baitoci guda biyu, daga cikin kasidarsa ta Arewa Jamhuriya ko Mulukiya, Mallam Saadu Zungur cewa yake: Mu dai hakkinmu gaya muku: Ko ku karba ko ku yi dariya, Dariyarku ta zan kuka gaba: Da nadamar mai kin gaskiya. Duk wanda ya san cikin garin Bauchi kafin shekaru shidan nan na mulikin Mai Girma Matawallen Bauchi, Malam (Dr) Isa Yuguda, ya san cewa garin Bauchi gari ne mai tsafta. Garin Bauchi yana cikin manyan biranen jihohi da kyan titunansu, da tsaftarsu suke burge mutane. Amma daga lokacin da Mai Girma Gwamnan Jihar Bauchi na yanzu, Mallam Dr. Isa Yuguda ya karbi ragamar mulkin Jihar, sai abin ya sauya a dalilin sabon tsarin kwashe shara da bola da gwamnatin tasa ta kawo, wanda ni a ganina tsari ne na shirme, tsari ne na gidadanci da kuma rashin azanci. Wannan mummunan tsari kuwa shi ne wai an tanadi motocin kwashe shara, da masu aikin kwasar sharar, don haka sai aka yi umurni ga mutane su rika fito da sharar gidajensu suna zubawa a bakin titi don motocin nan su kuma za su rika kewayawa suna kwashe sharar. To amma kasancewar motocin nan basu wadaci cikin garin yanda ya kamata ba, sai abin ya zama an yi, ba a yi ba. Ko kuma a ce, abin sai zama, baya ba zani. Bilhakika abin da ke faruwa shi ne, saboda motocin sharar sun yi karanci, to ba a samun kwashe sharar akan kari. Wannan ya sa sai ka ga shara a bakin titi ta yi kwana da kwanaki amma ba a kwasheta ba. Kuma mutane suna ci gaba da fito da sabuwar shara suna zubawa akan tsohuwar har sai ka ga bola ta habaka a bakin titi. Wannan shirin shudi na kwashe shara ya sa yanzu shara da bola sun zama manyan abin adon titunan cikin garin Bauchi, abin har abin kunya, idan mutum ya zo da baki garinsu. Yanzu haka, manyan titunan garin Bauchi wadanda da suke abin shaawa, sun zama wajajen baje kolin bola. Idan mai karatu ya gama karanta wannan bayani nawa, to ya dauki kekensa, ko mashin dinsa, ko motarsa, ko sayyadarsa, ya kewaya titunan Wunti, ko Kobi, ko Bakin Kura, ko Railway, ko titin Kofar Gombe, ko Kofar Ran, kai har ma gaban Fadar Mai Martaba Sarkin Bauchi zai ga tsibi-tsibi na shara, sai dai kuma gurin da aka yi sa-a an kwashe. Nan dinma, IDAN an Kwan biyu za a ga sharar ta sake taruwa. Abin da ya sa na ce wannan tsari akwai gidadanci tattare da shi shi ne, ita dai shara ko bola kazanta ce da ya kamata a boyeta ba a bayyanar da ita bainar jamaa ba. Abin da ya fi dacewa shi ne, a cikin unguwanninmu na cikin gari, gwamnati ta sayi kangwaye a cikin lunguna, ta killacesu a matsayin a wuraren zuba shara.n Saannan kuma sai ta buda hanyar mota zuwa kan kangon da ake zuba shara idan mota ba za ta iya shiga ba, don motar shara ta samu hanyar isa zuwa wajen. Inda kuma dama akwai hanya, to sammakal. IDAN aka yi wannan to an samar da permanent solution na kwashe shara(refuse disposal), kuma ba za a sake ganin titunan STATE CAPITAL dinmu da kazanta ba. Kuma Allah Shi ne Babban Shaida cewa tun ina cikin Gwamnatin Malam Isa Yuguda, na yi kokarin isar da wannan shawarar gareshi, amma bani da tabbacin ko ta Isa ga Mai Girma Gwamna ko bata isa zuwa gareshi ba, domin ba fuska da fuska na gabatar da ita ba. To amma zuwa yanzu, na ga tafiya ta yi nisa, kuma na ga cewa, idan fa ba a yi magana ba to wannan Gwamnati za ta tafi ta barmu da wannan jangwangwam din, ya sa na ce kai, turawa fa sun ce, BETTER LATE THAN NEVER. A gaskiya duk lokacin da na shiga garin Bauchi sai Raina ya baci saboda kazantar titunan nan da da babu ita, babu dalilin ta. A gaskiya wannan tsarin BAI YI BA. Wai yara Suka ce, da sakel. Kuma wannan sai ya tina mini da wata wakar kamfen da aka yi ma Mallam Isa Yuguda lokacin Yakin neman zabe, inda mawakin ya ke cewa, Bauchi albishiri, 2007 muka ce sai Isa, malami, masani, Gwamna mun zabi mai nazari. Ni dai a wannan tsari na kwashe shara, ban ga sani da nazari a ciki ba. ALLAH SA MU DACE. SALISU SHEHU-BUK.
Posted on: Sat, 19 Oct 2013 14:25:40 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015