ME YA FARU A KARBALA 12 Wasiyyar Muawiyah ga Yarimansa A lokacin - TopicsExpress



          

ME YA FARU A KARBALA 12 Wasiyyar Muawiyah ga Yarimansa A lokacin da sayyidina Muawiyah (R.A) ya lura da kusantowar ajali sai ya yi wasici ga wanda ya nada a matsayin magajinsa inda ya gaya masa maganganu masu tsadar gaske inda Allah ya sa Yazidu ya kiyaye su. A cikin wasicin nasa ne yake cewa, ka sani duk abinda na yi a duniya babu wanda ya kai hatsarin nada ka da nayi. Amma na yi ne ina mai kyautata maka zato. Idan ka kyautata zamu tsira ni da kai, in kuwa ka bi son zuciya to, lalle ne fa zamu sha wuya. Sannan ya yi masa wasici da kula da hakken marasa karfi da dai alamura da dama da zaku iya komawa gare su a littafinmu na Kaddara Ta Riga Fata. Game da wasicin da ya yi masa a kan sayyidina Husaini mun kawo maku shi a cikin wancan littafi daga littafan Sunnah amma shekaru goma bayan wallafa shi sai ga shi na yi tuntube da wata magana wacce ta yi daidai da waccan a littafin nan na Shia mai dinbin daraja a wurinsu. Don haka nake so in kawo ta a nan. Ga abinda Majlisi mai littafin ya ce: ووصى معاوية ابنه يزيد فقال له :- وأما الحسين فقد عرفتَ حظه من رسول الله، وهو من لحم رسول الله ودمه، وقد علمتُ لا محالة أن أهل العراق سيخرجونه إليهم ثم يخذلونه ويضيّعونه، فإن ظفرتَ به فاعرف حقه ومنزلته من رسول الله، ولا تؤاخذه بفعله، ومع ذلك فإن لنا به خلطة ورحماً وإياك أن تناله بسوء أو يرى منك مكروهاً Majlisi ya ce: Muawiyah ya yi ma dansa Yazidu wasici yana mai cewa: Shi dai Husaini ka san matsayinsa a wurin manzon Allah (S) (yana nufin kaunar da manzon Allah yake masa) kuma jininsa ne da tsokarsa. Ina kyautata zaton mutanen Iraqi za su fito da shi (da sunan tawaye) sannan su fita batunsa, su tozarta shi. To, idan haka ta faru kuma ka kama shi ka kula da hakkinsa da matsayinsa na wajen manzon Allah (S), kada ka kama shi da laifin da ya yi. Tare da haka kuma muna da kyakkyawar hulda da shi, ga kuma zumunta. Don haka, kada ka shafe shi da wani mugun abu ko ya ga wani abinda ba ya so a wurin ka. Duba Bihar Al-Anwar na Majlisi (44/311) To, ka gani fa. Wannan littafi na daya daga cikin manya manyan kundayen ilimi da tarihi wadanda Shiawa ke bugun gaba da su. Ga shi ya tabbatar da wannan wasici mai nuna cewa, babu wata gaba a tsakanin su irin yadda su yan shiah suke nunawa. Haka kuma ba shi nufin kome sai alheri gare su. Maganar zumunta da Muawiyah ya yi a tsakanin su kuwa yana da kyau wanda bai sani ba ya sani cewa, Banu Umayya dangin manzon Allah ne Sallallahu Alaihi Wa Alihi Wasallam. Domin shi Umayyatu kakan nasu dan Abdushams ne dan Abdumanaf. Abdumanaf kuwa shi ne kakan manzon Allah (S) na uku. Da Hashim kakan manzon Allah (S) da Abdushams mahaifin Umayyah uwarsu daya ubansu daya. Don haka ba mai raba Banu Hashim da Banu Umayya sai jahili ko kuma mai mugunyar manufa ga dangin manzon Allah makusanta. Kuma yayan manzon Allah (S) guda uku mata (Zainab da Rukayya da Ummu Kulthum) duk a cikin Banu Umayya suka yi aure. Kuma shi ne da kansa ya aurar da su. Fatima ce kawai ta auri dan uwanta Ali daga gidan Banu Hashim. A cikin gwamnatin manzon Allah (S) kuma babu wani gida da yake da kason da ya kai na Banu Umayya a cikin maaikata; gwamnoni da sauransu. Don haka, duk wanda yake jin yana kiyayya da gidan saboda yana ganin laifin wasu a cikin su to, ya canja matsayinsa. Zamu koma kan nadin Yarima bayan mutuwar babansa. Ku dakace mu.
Posted on: Thu, 24 Oct 2013 08:19:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015