***MUNAFURCI...2*** Hakika jiya na faro bayani dole na - TopicsExpress



          

***MUNAFURCI...2*** Hakika jiya na faro bayani dole na datse kasantuwar wayar bazata turo sakon duka ba. A ci gaba da jawo hankalin yanuwa wajen kiyaye wadannan Alamomi da yawa mutane na daukarsu ba bakin komi ba,wasu kuma suna ganin dan sunyi daya ko biyu daga ciki ai basu zama munafukai ba..hmmm ba haka bane kam domin kuwa ance sonsomin hauka?......... Saboda ma ka kiyaye Sayyidina Ali yaja hankalinka kamar yadda me akhdari ya kawo mana wani baiti haka: Thalathatu alamatul munafiq.......fakuz biha ya ibn akhee tuwaffiq. Alkazibu kulful ahdi thumma alhiq.......kul lal kiyanati fala tufarriq. Fahafiz ya akheel aqeelu.....alal wafai bil ahdi takun muhtaraman baina ikhwanika mauthuqan fi kalamika. Maana(Alamomin munafuki guda uku ne.....kayi riqo dasu yakai danuwana sai ka dace. Karya,saba alkawari,sannan ka riskar da dukkan alkhairi kada ku rarraba. Ka kiyaye ya kai danuwana me hankali,cikin cikawa da alkawari sai ka zamo abin girmamawa a tsakanin yanuwanka,sannan abin koyi a cikin kalamanka). Tabbas danuwa ko yaruwa idan muka kiyaye wadanndan darajar mu zata daukaka,dukda dai nasan ba kowane bahaushe ke gane dunqule ba,wani gashi bahaushe amma in akai wata hausar yana bukatar gwari gwari. Tom matsayina na autar dalibai zanyi bashinshi a dunqulenne amma da bayanin baitin kawai..ana son nuna mai lallai kiyaye wadannan alamomi gareka nada mahimmanci ta yadda zaka kiyaye kanka daga afkawa koda dayanzu ne,kada kace ai innai karya ta banbanta da saba alkawari sannan ba cin amana bane,aa lallai zaka jefa kanka tasku babu rarrabewa tsakanin ukun domin misalinka zai zama kamar wanda aka ajema Giya,mace da jariri ne ace kayi zina da ita ko ka kashe jaririn ko kasha giyar sai kaga ai duk wadannan shan giyar yafisu sauki ba tare da sanin fitar hankalin da zakai zai jefaka aikata duk sauran ba. Ya danuwana da yaruwa a musulunci idan muka kiyaye kanmu daga wadannan ukun zamu iya samun shugabanci me nagarta a nan gaba,domin rashin kiyayesu yasa shuwagabanninmu kashi casain da taran cikin su Munafukai ne,sannan ga jahilci da yai musu katutu domin duk wanda ya rasa ilmin addini shine shahili,shiyasa da zabe yazo zasu biku gidajenku suna manna muku karya da yaudara saboda munafuncin ya kamasu ga nufaqa a zuciyarsu sai ku amince dasu da sun hau kuma su hainceku. Tom gashi na gangaro amma dole inja burki anan...insha Allah a ci gabane nake fatan kawo mana makomar munafukai....dukkan kuskuren da zaku gani daga gareni ne daga shaidan abinda na fada dai dai kuma Daga Allah ne cikin amincewarsa...ina saurarar gyararrakinku.
Posted on: Wed, 04 Dec 2013 20:48:07 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015