MUTUM UKU DA DUNIYA TAKE JIRA SU ZO AYI TASHIN ALQIYAMA. - TopicsExpress



          

MUTUM UKU DA DUNIYA TAKE JIRA SU ZO AYI TASHIN ALQIYAMA. (1)-ISAH BN MARYAM (2)- MASIYHIDDAJJAL (JUJAL) (3)-AL-MAHDI................. BISMILLAHI-RRAHMANI-RAHIM. Wannan daya ne daga cikin rubutu da nayi a wani zauren.kuma zan cigaba da rubuto su. Kamar dai yadda muka sani alamun tashin Alkiyama ya kasu kashi biyu 2, akwai manya,sannan akwai kanana.daga cikin kanana manzon Allah(s.a.w) ya fade su acikin shahararren hadisinnan da umar bn khaddab(R.a) ya ruwaito. malaika jibril ya tambayi manzon Allah (s.a.w).sai ya zayya no su,yace:baiwa zata haifi uwar gijiyarta (maana yara zasu zo suna mulkin iyayensu,sai abinda suka fadi za ayi) kuma yace: za kaga(mutane) marasu takalma,masu yawo tsirara,talakawa tibis, suna kasar gina gidaje masu tsawo (gidan sama) sannan kuma ya fadi wasu a wadansu wurare banda wannan hadisin,daga ciki 1-mata zasuyi yawo tsirara,2-kwanaki zasu rika sauri,3-shi kansa aiko manzon Allah,alama ce ta tashin kiyama.4-sabon Allah zai yawaita.5-za aci amanonin mutane.6-yawait a zubarda jini,7- wanda yai riko da addini zai zama dan kauye agun mutane.8- zina zata yadu,kowane gida za a samu kayan kida,9-za ama masallaci kwalliya. Gaskiya kananan suna da yawa. immun samu lokaci zamu kara rubuta wadansu...........kuma duk wadannan abubuwan sun faru............manya ko ba a samu ko daya ba,dominko in aka samu daya, to duka sauran zasu biyo shi.domin abun kaman tsinkewan carbi ne...........to zuwan wadannan mutum ukun suna cikin manyan alamomin tashin Al-kiyama..............yanzu zan dauke su daya bayan daya zanyi baya ninsu. (1) J U J A L An sa mai suna masihi ne,saboda zai je ko ina aduniya banda maka da madina An amso hadisi daga Abu said (R.a)yace:manzon Allah (s.a.w)yace, jujal zai zo amma za a hana shi shiga Madina kuma,bazai iya shiga ba.amma zai yada zango awajen madina. Sannan za a samu wani mutum mafi alkhairim mutane,zai fito yace;na sheda kaine jujal dinda manzon Allah (s.a.w)ya bamu labari...har zuwa karshen hadisin...... SIFOFINSA 1-Zai bullone tsakanin sham da iraq,mutane zasu fara binshi daga isfahan. 2-Yahodawan isfahan sune zasu zama manyan mabiyan sa. 3-sannan kuma mata ne wadanda zasufi binshi. 4-Zai zo da ruwa da wuta. Wutan shine ruwan, Ruwan shine wutan. 5-ido daya yake da shi. A goshinsa an ru uta kafir ko kafara. 6-yanada sauri zaiyi tafiya da sauri sosai 7-Zai ce shi annabine.daga karshe yace shi Allah ne. 8-zai shiga ko ina aduniya banda maka da madina 9-zai rikayin ayyukoki irin na ubangiji, zai saukarda ruwan sama ga wadanda suka yarda da shi kuma zaice tsirai su fito kuma su fito. 10- zai yi kwana arbain, tsawon kwana dayan farko,kaman sheka,Rana ta biyu kaman wata,kwana ta uku kaman sati,sauran kwanakin kuma irin kwanakin mu. 11-matane zasu fi binshi. 12-kuma zai zone a shahararren...amma manzon Allah (s.a.w)bai karisa ba...ta iya yuwuwa yazo a shararran dan rawa ko dan kwallo ko makidi ko mawaki ko dai wani abu 13-akarshe annabi isah zai kashe shi. Allah ya tsare mu. Mutum na biyu da zamuyi magana akansa, annabi isah (a.s).
Posted on: Fri, 01 Nov 2013 20:14:00 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015