Matukar a AREWA da karuwai, yan daudu dasu da magajiya. Da - TopicsExpress



          

Matukar a AREWA da karuwai, yan daudu dasu da magajiya. Da samari masu ruwan kudi, Ga mashaya can a gidan giya. Matukar yayan mu suna bara, Titi da Loko-lokon Nijeriya. Hanyar birni da na kauyuka, Allah baku mu samu abin miya. Sun yafu da fatar bunsuru, Babu mai tanyonsu da dukiya. Babu shakka yan kudu zasu hau, Dokin mulkin Nijeriya. IN KO YAN KUDU SUNKA HAU, BABU SAURAN DADI, DADA KOWA ZAI SHA WUYA. A Arewa zumunta ta mutu, Sai karya sai sharholiya. Camfe-camfe da tsibbace tsibbacen, Malaman karya yan damfara. Sai karya sai kwambon tsiya, Sai hula mai annakiya. Ga gorin asali da na dukiya, Sai kace dan annabi fariya. Jahilci ya ci lakar mu duk, Ya sa mana sarka har wuya. Ya sa mana ankwa hannuwa, Ya daure kafarmu da tsarkiya. Bakunan mu ya sa takunkumi, Ba zalaka sai sharholiya Wagga alumma mai zata yo, A cikin zarafofin duniya. SAADU ZUNGUR - KUKAN KURCIYA
Posted on: Thu, 06 Mar 2014 21:28:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015