Mutuwa fa tana nan tana jiranka kamar yanda ta dauke maigidanka. - TopicsExpress



          

Mutuwa fa tana nan tana jiranka kamar yanda ta dauke maigidanka. Nima haka tana jira na kamar yanda ta dauke mahaifiyata. Saboda haka ina kira a gareka da "KAJI TSORON ALLAH". Bincike ya nuna cewa kashi tamanin daga cikin dari (80%) na matasan dake jihar katsina sunyi karatu shekara da shekaru amma basu da aikinyi, musamman ma wadanda sukayi karatu a bangaren lafiya. A cikin local government din da na fito akwai asibitoci da dama wadanda zaka je ka tarar mafi yawa daga cikin ma,aikatan yan casual ne, wani asibitin ma gaba dayanshi baka iya samun koda permanent staff guda daya, kai wani asibitin ma zaka iya zuwa ka tarar a rufe yake ba ma,aikaci ko daya. Mai girma gwamna tambaya agareka: (1) shin wai jiha bata da kudin da zata iya daukan ma,aikata ne? Idan akwai su to don me yasa baka dauka ba? Sannan kuma me ake yi da kudin wajen inganta rayuwar talakawa? (2) da hakan kake claiming din cewar kayi putting more emphasis akan prevention na maternanl and infant morbidity/mortality rate? (3) ina kungiyar ma,aikatan lafiya ne suke (MAHWUN) ko basu sanar da kai halin da asibitocin jihar ka suke ciki? (4) meye amfanin college of health sciences dake jihar ka? (SHT Daura, SHT Kanki,a, SMW Malumfashi da SN Katsina)? A rufe su mana! Tunda tun shekarar 1999 zuwa yau suke ta yaye dalibai amma 95% nasu har yanzu zaman kashe wando suke. (5) shin wai yanzu kana nufin naira dubu goma zata iya biyan bukatar rayuwar matashi har shima ya taimaka ma wani?. (6) mai girma gwamna wai ina masu baka shawara ne ko basu baka shawara ne akan abubuwa masu muhimmanci? Ko kuma kai din ne baka daukan shawarar?. (7) matasan nan idan baka iya daukansu aiki don me bazaka kirkiro masu da wadansu hanyoyi ba wadanda zasu iya dogara da kansu idan sun kammala karatu, Kamar yanda muka ga anayi a wadansu jihohi makwabtanmu? (ka dauki misali da jihar kano) =Matasan jihar katsina gareku. Naj barku da sauran tambayoyin ku tambaye shi da kanku.=
Posted on: Wed, 31 Jul 2013 11:02:27 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015