NAMIJI KANIN ALJANI.....KASHI NA 3.......Maryam ta cigaba da cewar - TopicsExpress



          

NAMIJI KANIN ALJANI.....KASHI NA 3.......Maryam ta cigaba da cewar abin dayasa kukaga hawaye na fitowa daga idanuna , idan na tuna da wasu abubuwa guda 2 wayanda bazan taba mantawa dasu arayuwata ba, aduk lokacin dana tuno dasu duniyar nan takan zamemin duhu, duk wani nauz,in farin ciki sukanyi kaura daga gareni nakan shiga yanayin damuwa mara misaltuwa!!! Har wasu lokutannakanji kamar in kashe kaina domin banga amfanin zamana nan duniya batare dasu ba, duk lokacin da wannan tunani yazomin nakantuna da makomar musulmin da yakashe kansa, duk musulmin kirki yayi imani da kaddarar alkhairi data sharri wayan nan abubuwa 2 bawasu bane illa mahaifiyata aduk lokacin da natuna da ita da irin mutuwar bakin ciki datayi yakan sake sani tsanar mahaifina nakan shiga yanayin rudani mara iyaka abu na2 da yake kara tayar min dahankali, yakan sa inwuni zub da hawaye nakakasayin komai domin nakan tuna da ranar babban farin cikin mu daga bisani yakoma bakin ciki shine farin cikina, ruhina, jigon rayuwata,gatanashine wanda yazame min haske lokacin danake cikin duhu, shine wanda yazame min farin ciki lokacin danake bakin ciki, shine wanda ya soni a lokacin da kowa yake kina, wato mmmmmmm......,,, muryartace takama rawa sannan wani sabon kuka yakara barke mata wanda har yafi na farko sai da yajanyo hankalin goggo mai abincin gayu kallon wajen da suke zaune tayi da sauri ta taso gata ta kware wajen iya masifa tafara da cewa kajimin yaran zamani da iya shege tana cikin zaman zamanta lafiya lau kunzo kunsata kuka me kukayi mata kunsan irin alherin da take dashi kuwa kunji yara zasu jawomin ma.... Maryam tashi kawai tayi tafita da gudu daga cikin shagon abincin tsaye motar take wanda ba wanda yasan cikinta kasancewar bakaken gilas ne jikin motar . Fitowar ta ke da wuya ta nufi tsallaka titi zuwa inda tayi parking din tata motar goggo mai abincin gayu ta cigaba dayi musu masifa da cewa ga irinta nan ai abincin ma kun hanata ci ballantana tayimin alherin da tasaba yimin sai kun b,,,,,,,,,, karar ihun da sukaji ne yasa sukayi waje da gudu domin gane wa idon su abin da yafaru maryam sukagani kwance cikin mawuyacin hali sannan suka mai da dubansu izuwa motar databige maryam domin ganin wanda yayi wannan aika aika amma basu iya gane komaiba kasancewar bakace sannan bakakengilasne jikinta ba plate number balle su dauki number motar har motar ta sha kwana suka daina ganinta batare da sunsami makama da zasu iya gane motar ko mai motar ba Dr abdulazeez babban likita ne wand ya kware wajen gudanar da aikin sa kusan ince duk likitoci sa annin sa girmamashi sukeyi domin finsu iya aiki dayayi nesa ba kusaba Dr a-z ne kanta domin ceto rayuwarta daga mawuyacinhalin da take ciki sai da aka sami kusan sa,a 3 sannan maryam ta farfa do daga dogon suman datayi bude idonta ke da wuya ta kwalla wani uban kara waiyo nashiga uk,,,,,,,,,,,,,,,,,next episode [[Aminullah05]]
Posted on: Fri, 21 Jun 2013 20:37:35 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015