NASIHAR MU TA YAU 13. MALAM ABDULLAHI bn MUHAMMADU bn USMANU bn - TopicsExpress



          

NASIHAR MU TA YAU 13. MALAM ABDULLAHI bn MUHAMMADU bn USMANU bn FODIO yaci gaba da bamu shawarwari kamar haka: Ya kai bawa! Kana ta zaton zaka shiga kabari amma ga zahiri ka kaurace watau aikin ka bai nuna da gaske kake kasan zaka shjga ba. Jikinka jikin rayayye amma zuciyar ka ta manta da wadanda ke cikin kabari. To kayi gaggawa ka dawo zuwa ga daar Allah. Wallahi jikin ka baya iya jure ma wuta, da zugazugi fa ake hura ta! Ka lizimci kofar Ubangijin ka wata kila a bude maka. Muna fatar kila Allah ya tarfa ma garika nono. Amin. Da yawa daga wanda rana ta fito ya wayi gari yana farin ciki, amma ba zata fadi ba sai yana cikin kabari. Ya kai rafkananne! Za kayi nadama yayin da aka busa kaho ka tashi zuwa makomar ka. Ya kai wanda duniya ta rude shi, ina ma dai ace ka tilasta ma kanka tuba da kokon zuciyar ka wanda ya karye. Kayi riko cikin dukkan halullukan ka ga wanda gare shi lamurra suke komawa. Ya kai wanda yake bacci kamar wanda yake farke! Nisan milamilai nawa ke tsakanin ka da salihan bayi? Ina masu karfi da mayaka da masu mulki? Shin yan uwanka nawa ka dauke su ka raka su makabarta? To ka nemi guzurin wannan tafiyar don kaima sai kayi ta! Ka tsaya kana aikata abinda kaga dama kamar dai kai mutuwa ta kyale ka! To Wallahi kada ranka ya rudeka saboda amincin da ya baka, kaga kana da karfin jiki ka 6ata rayuwar ka wajen saye da sayarwa ko amsa da bayarwa. Allah SWT yace; Kowace rai mai dandanar mutuwa ce. Kuma zaa baku ladar ku ranar alqiyama, duk wanda ya tsira daga wuta kuma ya shiga aljanna to wannan ya samu babban rabo, kuma rayuwar duniya bata zamo ba face jin dadi ne dan kadan na rudi. Allah muna rokonka ka shiryar damu hanya madaidaiciya, kayi mana gafarar zunubban mu wadanda kuma yi da wadanda zamuyi nan gaba, kasa mu cika da imani, ka saukaka mana mutuwa, ka sanyaya mana kwanciyar kabari, ka tada mu cikin inuwar ka ranar alkiyama, ka tserar damu daga azabar wuta, ka sanyamu cikin ceton Annabi SWA, sannan kasa mu aljannar firdausi don Annabi da Alqurani amin.
Posted on: Sun, 10 Nov 2013 07:23:04 +0000

Trending Topics



style="margin-left:0px; min-height:30px;"> In a world of New Age religions, Logistics, and Non Believers many
United States Air Force, DLA complete historic fuel
Holiday Deals BagBowl 8 Piece Food Storage Starter Set Christmas

Recently Viewed Topics




© 2015