/NISHADANTARWA/ Wasu samari ne guda 2 abokan juna, dayan yayi - TopicsExpress



          

/NISHADANTARWA/ Wasu samari ne guda 2 abokan juna, dayan yayi karatun boko, shi kuma dayan baiyi ba.......... Wata rana suna zau ne a bakin titi, sai sukaga wata kyakkyawar yarinya ta taso daga makarantar bolo tana rike da littafai a hannunta. Sai wannan saurayi da bai yi karatun # BOKOba yaji yana son ya tsayar da ita amma kuma yana tsoro, sai ya tambayi abokinsa wanda yayi karatun #BOKO akan idan yaje wajanta mai zai fada mata da turanci! Abokin sa yace, in kaje farko kace mata HELLO idan ta amsa sai kace mata SLAP ME PLEASE! ko mai tace maka kace mata YES!!....Haba! Nan fa gayen ya tashi yana kwambo ya yi wajan yarinyar abokin yana taka masa baya, ya ga yadda firar tasu zata kasance. # Saurayi: Hello! (yana murmushi yana kwambo) # budurwa: Hy! #Saurayi: slap me please #budurwa: slap ????? #Saurayi: yes #budurwa: nan sai da ta dage ta zafga masa mari a fuska. Ya dafe fuskar sa yajiyo wajan abokinsa yace masa mari nafa tayi shi kuma abokin sai yayi murmushi yace: turancin yafi karfinta ne, ta kasa gane me kake nufi, yanzu kace mata SLAP ME AGAIN....Gayenka sai ya juyo wajan budurwa yace: Slap me again!! Ita ko ta sake sharara masa mari, cikin fushi n ya juyo ga abokinsa yace: Babaa, anya tanajin turancin kuwa?? Shi kuma abokin sai yace: burga take mana, ba turancin da ta iya, sokuwa ce! Ya kama hannun abokin suka juya suka tafi... Wai in kaine saurayin da aka mara ya zakayi da abokin nan naka???
Posted on: Sun, 01 Dec 2013 21:02:34 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015