RASHIN SANI Part one - 1 Nidai suna na sumayya, amma mutane sunfi - TopicsExpress



          

RASHIN SANI Part one - 1 Nidai suna na sumayya, amma mutane sunfi kira na da sumy baby, Allah yayimin baiwar kyau sosai, kasancewar mahaifiyata yar fulani ce, ni kuma ita na biyo, farace ni doguwa, bangaren samari kuwa, ba,a magana, a kalla samari na, sunkai guda 20, amma acikinsu na zabi guda daya, mai suna ahmad, sauran kuma duk na koresu, na hanasu zuwa gurina, Ahmad, saurayine dan shekara 28, ya kasance mai kudine sosai, bugu da kari kuma kyakykyawane shi, sosai, to wadannan abubuwa sune suka sa na zabi ahmad a matsayin wanda zan aura, duk wanda yaga irin soyayyar da mukeyi da ahmad, abin sai ya burgeshi, a kullum burina kawai naga na zama mata a gareshi, sana,ar ahmad kuwa, yana sayo kayane daga wasu garuruwan yakawosu zuwa nan cikin garin kano, wata rana ahmad yazo gurina da misalin karfe 09:30pm, ina zuwa yake fadamin, an dauko kayansa daga garin lagos, anzo daidai wani gari mai suna niger, daidai wata gada, da ake kira, jaba, motar ta fadi, kuma ta kama da wuta, kurmus ta kone, kayan da suke cikin motar sunkai kimanin na naira miliyan dari biyar. A lokacin da yagama fadamin, saida naji jiri yana dibana, saura kiris na zube kasa, gaskiya na tausayawa ahmad sosai, nan dai kawai yatafi ya barni, ina ta tunani, na shiga gida, naje na kwanta, amma na kasa bacci, ina ta tunanin kasancewar rayuwata, washe gari na shirya da wuri, na tafi gidan su kawata sadbaby, ina shiga gidan sai na tarar da mominsu a tsakar gida, ai kuwa na gaisheta, sannan nace mata sadiya tana nan kuwa? Tacemin tana cikin dakinta, nashiga dakin sadiya, tana gani na ta taso da murna ta rungumeni, tana cewa, kawata lafiya kuwa? Na ganki da sassafe yau a gidanmu? Tayi dogon numfashi, sannan tace mata, mu samu guri dai mu zauna kawai, suka zauna a gefen gado, sumy ta bata labarin duk abinda yafaru da ahmad, sadiya ta danyi jim!, sannan tace mata, to ke wacce shawara kika yanke? Tace gaskiya nidai na yanke shawarar rabuwa dashi, sadiya tace, gaskiya kinyi dabara mai kyau, kinga dai na farko, ke kyakykyawace, ba zaki taba yin kwantaiba, nan dai suka tafa, sannan sukayi shewa, sumy ta koma gidansu, lokacin da dare yayi, ahmad yazo gurin sumy, tana fitowa kuwa, ta fara yaba masa maganganu, sannan ta kara masa da cewa, yanzu bazan iya aurenka ba, dan haka kada ka kara zuwa gurina, idan kuwa kazo to duk abinda nayi maka kaine ka ja, mtsww, haka kawai tayi, sannan ta juya, ahmad yayi ta kiranta amma taki juyowa, dare yayi sosai da misalin karfe 02:15am na dare, sumy tana kwance, kawai sai taji........... ....
Posted on: Thu, 19 Sep 2013 20:12:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015