RUWAN BAGAJA Tallifin alhaji abubakar imam na farko Am fara - TopicsExpress



          

RUWAN BAGAJA Tallifin alhaji abubakar imam na farko Am fara bugawa 1984 A cikin farkon zamanin shaihu dan ziyyazanun an yi wani muutum motsatsyse, wanda a ke kira koje sarkin labari. Dalilin da ya sa a ke kiransa haka, don haukansa ba na zagin kowa ba ne, ba kuwa na dukan kowa ba ne. Shi dai ba abin da ya ke so sai yaji labari, ya tafi wadansu kasashe, ya rika ba attajirai da sarakuna, su kuwa suna ba shi abinci. Inya ba ka labari, wanda ba ka sani ba , inka ba shi kudi sai ya debi hamsin ya ba ka. Ya tsare ka, ya ce kai kuma sai ka ba shi wani. Wanda shi kuma bai sani ba. Yana cikin bin kasashe, har ran nan allah ya sa ya isa wani gari wai shi kwantagora, wani babban birni ne a cikin kasar sudan. Ya isa wajen sarkin garin, aka kai shi masauki. Da ajiye kayansa, sai ya fito kofar fada, ya shiga halibsa na neman labaru da ba da su. Ya kwana uku yana ba sarki labarurruka, fadawa kuwa suna biyansa da wadansu labaru, watau maimakon wadanda ya ba sarkinsu. Sarkin kasar ana kiransa sarkin sudan. Yana yawo cikin gari, sai ya isa wani katon gida mai benaye da yawa. Ya tambayi barorin da ya tarar zaune ya ce, shin gidan wane ne wannan? Suka ce, wane ne duk duniyan nan bai san alhaji imam ba? Koje sarkin labari ya ce musu, yana fitowa yanzun? Suka ce, wa zai fito da shi yanzun tun azahar ba ta yi ba? Koje ya share wuri, ya zauna kan azahar ta yi. Azahar na yi, sai suka ji taf taf taf, duk zaure aka dubi maigida ya shigo aka yi gaisuwa. Da ya zauna ya dubi koje ya ce, wannan fa wane ne? Koje ya ce, ni ne sarkin labari. Yau kwanana goma nan garin. Kaji kaji safarata ka kuwa ji yadda ake biyana, ko kana iya saye? Maigida ya ce, to fadi muji. Yau allah ya gama ka da gamonka. Koje ya yi murmushi ya ce, to sai dai mu ce allah ya gama kowa da gamonsa. Sa an nan fa koje sarkin labari ya tsunke. Ya yi ta zuba labaru, ba wakafi balle aya. Da ya fadi kaman talatin sai ya ce wa magida, biya wadannan tukun, sa an nan in ji karfin ci gaba. Maigida yace, kara dai! Ya yi ta zubawa , har allah ya gajishe shi. Da ya kare, zuwa magriba, sai maigida ya ce, to duk kai labarunka ashe ba su fi a ba da su ba daga safe zuwa magriba ba, har ake kiranka koje sarkin labari? Kuma ya ce masa, to gobe ka zo da kai da abokananka duka, ni kuma in ba ka labarin abubuwan da na yi a duniyan nan, in na yi kokari in gajarce labarin koma ko ma kare cikin kwana gima? Koje sarkin labari ya duka ya yi ban kwana. Gari na wayewa sai ya taho ya zauna yana jiran maigida. Can zuwa fitowar rana ya fito, mutane da ke zaune a zaure suka yi masa barka da kwana. Ya hhaye kujerarsa ya kame, ya dubi koje yace, jnnenka nawa
Posted on: Thu, 03 Oct 2013 16:27:54 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015