*SAURAYINA YA KASHE MINI AURE* Don Allah addmin ku boye - TopicsExpress



          

*SAURAYINA YA KASHE MINI AURE* Don Allah addmin ku boye sunana wllh ina cikin mawuyacin hali wayyoni ! Tun ina SS 2 muke tare dashi, muna soyayyah amma ni gaskiya ba sonshi nake ba, kawai de dan shine ya fara cewa yana sona, kuma mun riga mun saba bazan iya korar saba, amma ni ban taba son shiba, ban taba sha,awar ya zama mijina ba, a lokacin dana gama scndry sai iyayena suka ce na fito da miji. Nan fa hankalina ya tashi na samu guy dina na sanar dashi amma saiya cemin shi gaskiya ba aurene a gaban saba karatu yake yi, nayi hakuri na jirashi zuwa wani lokaci. Na sanar da iyayena suka ki yarda, ana haka sai kawai wani mutun yazo gun Dad dinmu yace yanason aure na, haka suka aura min aure da mutumin nan badan ina so ba. Saurayina yayi kuka, kamar me, duk da ba sonshi nake ba amma nima saida nayi kuka sosai, har rashin lfya nayi sbd na tausaya mai, haka de muka yi bankwana aka daura min aure. Wata rana da safe muna tare da mijina muna hira kawai sai wani yaro ya shigo ya miko min wata leda yace gashi inji guya dina *ya fadi sunan shi* wai zaizo anjima, bansan mene a ciki ba, mijina ne yayi sauri ya karbi leda, yana budewa, saiga condom parket, parket, nan fa hankalina ya tashi, kafin nayi magana mijina ya fice daga gidan, ranar bai kwna gidan ba. Yanzu haka duk ya canza min ya dena kula ni, na rantse masa ni bansan zancen ba amma wlh yaki yadda gshi kullum sai barazanar zai sakeni yake, frds ku taimaka min ya zanyi ?? by ahmad a baba
Posted on: Tue, 29 Oct 2013 17:05:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015