***SHANYAR MAHAUKATA***** SHANYAR MAHAUKATA A asibitin mahaukata - TopicsExpress



          

***SHANYAR MAHAUKATA***** SHANYAR MAHAUKATA A asibitin mahaukata ne, wani mahaukaci mai suna dankawu ya tsunduma cikin wani katon tankin ruwa, wani mahaukacin, wai shi mudi ya hango shi yana neman mutuwa, sai, nan take ya je ya tsamo shi jin wannan labari sai babban likitan asibitin ya zaci cewa lallai mudi ya warke, kuma ya kamata ayi masa dubawar karshe a sallame shi, likita ya kira shi yace: amma fah mudi ka burge ni yadda ka tsamo dankawu daga tankin ruwa ka ceci ransa, saboda hak.... kafin ya karasa magana, sai ga wani a guje yana cewa: ai dankawu ya rataye kansa ya mutu jin haka sai mudi ya ce: kash! Wallahi ba kashe kansa ya yi ba. Ni ne na rataye shi dan ya bushe, bayan na tsamo shi daga tankin ruwa!.
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 19:39:05 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015