SHEIKH IBN QAYYIMUL JAUZIYYAH (Rahimahullahu) yana cewa: ABUBUWA - TopicsExpress



          

SHEIKH IBN QAYYIMUL JAUZIYYAH (Rahimahullahu) yana cewa: ABUBUWA HUDU SUNA BUSAR DA FUSKA: 1) Qarya 2) Rashin kunya 3) Tambaya ba don neman Ilmi ba (Tambayar Qure). Yace: ABUBUWA HUDU SUNA QARA HASKEN FUSKA: 1) Tsoron Allah 2) Cika Alqawari 3) Mutunci 4) Karamci. Ya cigaba da cewa: ABUBUWA HUDU SUNA KAWO ARZIQI: 1) Yawan tsayuwar dare 2) Istigfari lokacin sahur 3) Yawan sadaka 4) Yawan anbaton Allah a farkon dare da Qarshensa. ‘Yan‘uwa mu dage! Ba a samun abinda ke wurin Allah na ni‘ima sai da biyayya a gare shi. ALLAH ya bamu ikon gyara ayyukanmu, ya Qara mana Imani ya kuma tsare mana shi, ya tabbatar damu akan tafarkin shiriya, mu rayu mu mutu akai domin tsarkin sunayensa. (Ameen) #AIY
Posted on: Sat, 07 Sep 2013 05:28:36 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015