SHIN KO KUMA KUNGA YAN SHIA SUNA YAWO DA BAKAKEN KAYA? TO GA - TopicsExpress



          

SHIN KO KUMA KUNGA YAN SHIA SUNA YAWO DA BAKAKEN KAYA? TO GA YANDA ABIN YAKE A wani shiri mai sunaTambaya Mabudin Ilimida aka watsa kaitsaye a yammacin jiya Litinin, a tashar Rediyon Tarayya (PYRAMID FM) da ke Madobi-Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da ke zaman babban bako a shirin, ya bayyana cewa babu wata rana (indai a shariar addinin musulunci ne) da aka ware, aka ayyanata cewa duk lokacin da ta zagayoranar bakin cikice. Ranakun da kawai ake wa irin haka, su ne ranakun farin ciki kamar na idin sallah babba da karama. Amma in dai a wannan addinin namu ne na musulunci, wanda Allah Ya aiko ManzonSa da shi zuwa garemu, kaf cikar addinin babu inda aka taba ayyana wata rana don ta zama duk lokacin da ta zagayo sunantaranar bakin ciki. Kuma in da za a yi hakan, to babu shakka da ranar da Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam ya bar duniya ce ta fi dacewa da haka; don a ranar ne alumar musulmi sukai bankwana da ran wanda ya fi kowa alheri a duniya. Haka in maganar kisa ne, manyan Sahabban Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam irin su Sayyidina Umar, da Sayyidina Usman, da Sayyidina Ali duk kashe su aka yi. Kai kafin zuwansu ma, Littafin Allah (Alkurani maigirma) ya bamu labarin cewa an kashe wasu Annabawa. Amma babu wani umarni daga Allh ko MaaikinSa dake nuna a rika mayar da ranakun barin wadannan manyan bayin Allah duniya, su zama ranakun da za a rika rayawa da ibadarbakin ciki. Magana ta zahiri dai, duk wadanda suka kashe babban mutum kamar Jikan Manzon Allah sallallahu alaihi wa alihi wa sallam wato Sayyidina Hussaini, tsinannun Allah ne. To amma wajibi ne ka tsayar da kanka a bayanshariakana biye da ita. Maimakon ka shiga gabanta ka tsarawa kanka wani biki da zai rika maimaituwa duk shekara nabakin ciki. In ko za kai haka, to dole sai ka zo da inda ka samo umarnin kebe ranar da sanya wani launi na tufafi, da fitowa ai zanga-zanga akan tituna, wanda duk da muhimmancin Annabawan da aka kashe a tarihin wannan addini, ba mu taba jin Manzon Allah Ya taba yin irin wannan biki da kuke yi, a ranar da daya daga cikin wadannan Annabawa ya bar duniya ta zagayo ba. Lallai da a ce duk wani mai daraja da aka kashe, dalili ne cewa idan ranar ta zagayo a hana kai sakat, a wuni a kwana ana bakin ciki sanye da bakaken kaya, da kusan a duk kwanakin shekara za ai ta ibadarbakin cikine; domin kullum baka rasa wani babba mai daraja a gun Allah da aka taba kashewa a tarihin ranar. Kuma idan kai a gunka ba abin girmamawa ba ne saboda bambancin fahimta, wani a gunsa yana da girma. Haka za ai ta raya wadannan kwanaki nabakin cikihar tsawon shekara, wanda hakan kuma ya sabawa tsarin da addinin musulunci ya zo da shi. Ga Allah daishiriyatake. Rokonmu kuma har kullum Allah Ya dawwamar da mu a cikinta. Ameen Daga: Sahabi Usman Abdallah
Posted on: Tue, 12 Nov 2013 20:06:48 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015