SON ANNABI (saww) DA GIRMAMA SHI SHINE RUHIN - TopicsExpress



          

SON ANNABI (saww) DA GIRMAMA SHI SHINE RUHIN IMANI.. ****************************** Tabbas wannan zance haka yake. Domin kuwa soyayya da girmamawa suna kaiwa izuwa tsananin biyayya.. Irin Wannan soyayyar da girmamawar itace tasa Sahabbai suka samu Tsantsar biyayya ga Fiyayyen Halitta.. Wannan yasa suka zama mafiya cikar imani acikin jinsin Yan Adam (In banda Annabawa alaihimus-salam) Wai sai kaji wasu suna cewa Bin sunnar Annabi shine kadai son Annabi (saww) Masu wannan jawabi sunyi wa kalmar mummunar fahimta.. Bin Sunnar Annabi (saww) abu ne mai mutukar muhimmanci, kuma babban ginshiki ne acikin addini.. Amma kuma ba shi kadai ne hanyar son Annabi ba.. Sai dai yana daga cikin alamomin son Annabin (saww).. Ga wasu misalai da zan bayar domin afahimci manufata. 1. Zaka iya yin biyayya ga mutumin da kake Qauna, harma wanda baka Qauna.. 2. Amma mutukar kana son mutum, so na hakika, To dole ne zaka tsinci kanka acikin ya masa biyayya ba tare da ka sani ba ma.. Saboda Qarfin soyayya idan ya kama zuciyarka, yakan janyo gangar jikinka izuwa ayyuka na biyayya akowanne lokaci.. Shi yasa Maulana Shaikhul-Islam (ra) yake cewa: IDHAA SAARA KHAIRUL-KHALQI SIRTU WARAAAHU... IDHAA HALLA YAUMAN, FAL- MASEERU BAEEDU. Acikin Tarihin Maaiki (saww) an samu halittu da dama wadanda suka samu darajoji da muqamai awajen Allah da Manzonsa (saww) ba tare da sun taba yin sallah ko azumi, ko kuma wani aikin lada ba.. Aa Sai dai Domin sun nuna SOYAYYAR MANZON ALLAH (saww).. MISALI: 1. DUTSEN UHUDU:- Manzon Allah (saww) yana cewa Uhud dutse ne Wanda YAKE SO NA, nima kuma INA SON SHI. Kunga kenan dutsen Uhudu ya rabauta.. 2. KUTUTTUREN DABINO:- Wanda yayi kuka saboda tsananin Shauqi da Qaunar Annabi (alaihis-salam).. Kuma Annabi (saww) ya yarda dashi.. Gashi anan duniya amma yana chan Annabi ya dasa shi agidan ALJANNAH. 3. BURAQAH:- Wacce ya hau adaren ISRAI DA MIIRAJI.. Ta kasance acikin Yan uwanta Burakoki, amma ta rame bata ci bata sha saboda tsananin Bege da tunanin Annabi (saww). Shi yasa Malaika Jibreel (as) ya zabo ta ya taho da ita domin taga MASOYINTA (saww). Kuma kafin ya hau bayanta sai da ta nemi wasu alfarmomi guda biyu awajensa (saww). TACHE: Ya Jibreelu ka gaya ma Wannan Masoyi, maabocin fuska mai kyau da Qyalkyali, INA SO YA SANYA NI ACIKIN CETONSA.. KUMA INA SO YA LAMUNCE MIN IN ZAMA ABIN HAWANSA AFILIN ALQIYAMAH. Nan take MANZON NAMU (saww) yace NA LAMUNCE MIKI. 4. TAKALMINSA (SAWW): Takalmi mai daraja. Shugaban dukkan Takalma.. Takalmin da yaje har Saman sama ta bakwai. Takalmin da yaje wajen da duk wata halittar Allah bata je ba. Takalmin da ya taka SAMAN ALARSHI. Takalmin da yaje wajen da babu sama babu Qasa. Babu haggun babu dama. Babu gabas babu Yamma. Babu dare babu rana. Babu yanzu babu Dazu. Babu Akwai babu BABU.... TAKALMIN DA YA KETA HIJABAI.. Yaje har kan SHIMFIDAR KUSANCI.. (hmmmm....... bari inyi shiru dai)... 5. SANDARSA (saww) wanda ya baiwa wani Sahabinsa lokacin da yayi wata bajinta. Har yace masa KAZO MIN DA ITA ARANAR QIYAMA NI KUMA ZAN SANYA KA AGIDAN ALJANNAH 6. KOGON DA YA SHIGA: Aranar yakin Uhud.. Har yanzun nan Kogon yana Qamshin jikin Maaiki (saww). Kai wallahi List din yana da tsawo domin kuwa abubuwan suna da yawa ba zasu lissafu ba.. 7. QISSAR MUTUMIN NAN: mashayin giya wanda aka yi masa haddi har sau biyu. Da yazo akaro na ukun sai Sayyiduna Umar zai tsine masa. Sai Manzo (saww) yace KYALE SHI YA UMAR. HAKIKA SHI YANA QAUNAR ALLAH DA MANZONSA.. Mu dai Ya Allah muna tawassuli da ZATIN MANZON ALLAH (saww) da siffofin na nasa da halayensa wadanda kyawunsu basshi kwatantuwa, Ya Allah Azurta mu da TSANTSAR QAUNAR MANZONKA (saww).. Mu mance kowa mu mance komai sai SHI (SAWW).. YA ALLAH ka azurta mu da tarayya dashi zahiran wa batinan.. Fid-dunya wal- Akhirah.. Sallu alaihi wa sallimu tasleeman admin Nuraddeen Nuhu
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 19:11:12 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015