TA KAWO MUN ZIYARA TA MUTU A DAKINA !!! Kamalu dan gaye ne - TopicsExpress



          

TA KAWO MUN ZIYARA TA MUTU A DAKINA !!! Kamalu dan gaye ne wanda duk wadanda su ke hulda da shi sun shaida hakan,wannan ne yasa wasu daga cikin abokansa su ke kiransa da sunan ajibota ,kamalu yana karanta biology a jamiar Ado Bayero da ke garin kano,yana da wata budurwa da ake kira da Fiddausi amma an fi kiranta da feedi.wata rana bayan sun yi hutun zangon farko na shekararsu ta biyu a jamia ,sai feedi ta ke shaida wa ajibota cewar za ta kawo masa ziyara amma ba tare da ta sanar da gidansu ba,. Feedi yar jahar Kaduna ce wadda ta gagari iyayenta. Kwatsam wata ranar jumaa sai feedi ta yi wa gidansu karyar cewar za taje gidan yarta ta wuni dake unguwar Dosa a cikin garin kaduna.A ka ko barta a gidansu, da fitar ta daga gida ba ta zame ko ina ba sai tashar mota, ta hau motar kano, tafiya sannu-sannu har Allah ya kawo su kano,tana sauka tun a tashar mota ta sa hannu a jaka ta dauko babban hijabi har da nikafi ta saka kasancewar suna da yan uwa a Kano kada su ganta su yi waya,nan take ta kira Ajibo a waya shi ko jikinsa na rawa don murna yazo ya dauke ta a babur dinsa ,ba su tsaya ko ina ba sai unguwarsu wato gwammaja,da zuwansu ya bude dakinsa feedi ta shiga shi kuma ya wuce ya nemo musu kayan sanyi(soft drinks) ,da ya dawo feedi ta tashi ta rungume shi har da sumbatarsa su ka zauna suka yi ta hira har tsawon wani lokaci.misalin karfe uku na rana sai ajibo ya dan tashi ya shiga gidansu,feedi ko tana zaune a dakin da fitarsa sai ta ji kanta ya fara ciwo, sai ta dan kishingida kwanciyarta kenan tace ga garinku,can sai ga Ajibo ya shigo da saurinsa yana kiranta cikin gadara Feedi! Feedi !shiru ka ke ji ,sai ya ganta a mimmike nan fa hankalinsa ya tashi yaje ya taba wuyarta ya tabbatar ta mutu,nan fa ya fara gumi ,ruwan kansa ya kare,ya ji ya fara jin fitsari anan take kuma yana cin bayan gari,wata zuciyar kuma tana hikayo masa zaman gidan yari har ya mutu ,nan fa Ajibo ya fara hawaye.Ajibo na nan a tsaye har karfe hudu na yamma ya rasa abinda yake masa dadi can sai ya ji kamar yana jin bayan-gari sai ya kewaya sai ya ji sam bai ji, haka dai ya zauna sai gumi yake idonsa ya yu wuri-wuri sai sake -sake yake a zuciyarsa yadda zai yi ya fidda kansa. Wata zuciyar ta na ce da shi ya fada wa mahaifiyarsa, wata zuciyar kuwa tana ce da shi kawai ya bi dare ya ajiye ta a bakin titi ba tare da kowa ya gan shi ba,yana cikin haka sai ya ji wayarta tana karan shigowar sako, yana dauka sai ya ga,an rubuta , KI YI MA ZA KI DAWO GIDA BABANKI YANA NEMANKI SAI FADA YAKE. yana duba lambar sai ya ga my momy,nan fa ya kara rikicewa sai ga hawaye suna zuba daga idanuwansa. Kan sa ya ya kuma kullewa tunaninsa ya kare ga yamma sai yi ta ke. Rayuwar Matasa a Yau Rayuwar Matasa a Yau Ajebo na nan zaune a daki cikin zulumi ga kuma wayarta sai faman kara ta ke, kawai sai ya yi ta maza ya kashe wayar, nan take kuma wata shawar ta fado masa na yaje a buga masa akwatin katako kawai ya bi dare ya je ya jefar da gawar a wani waje nesa da unguwarsu,haka kuwa a ka yi, nan take ya yi wani farat kamar an ce da shi ta shi, yadauko kwado ya kulle dakinsa ya fito jikinsa a sanyaye, ya ciro wayarsa ya kira yaseer abokinsa yana yake yana ce masa kai wa ya gaya ma an gan mu da feedi, bayan ko waya da ita ba ma yi kwanan nan, sai yaseer ya amsa cikin dariya yace zolayarka nake ajeebota ,ai nasan da tazo za ka neme ni mu gaisa,nan fa ya dan ji sanyi a ransa.Da zuwansa yan katako ya biya aka buga masa akwati babba, bai dauko ba sai misalin goma na dare kafa ta fara yankewa ,bai iso dakinsa da akwatin ba sai misalin karfe sha daya na dare ,da shigarsa dakin yasa sakata ya kulle, ya dauki hijabin da ta sa ya sa mata shi a jikinta ,ya dauki wayarta ya goge bayanai na kiran wayar duka(call information).yana nan zaune ya jira dare ta raba,amma kuma zuciyzrsa cike da fargaba,canwajen karfe daya da minti arbvain na dare sai ajeebo ya suntumi akwati a kansa sai tafiya ,ya tafiya mai tsawo sanna nan ya bi wasu yan luguna da kar akwai wanda yake biyo shi a baya,har daya iso wata unguwa wai ita Sharada da isar sa sai ya samu wata mahada na titi(junction ) ya ajiye akwatin ,ya bude ya ciro gawar ,ya ajiye ta a wajen,sai ya daiki akwatin ya tafi can gaba ya kunna wa akwatin wuta, ashe duk abinda yake yi tun isowarsa akwai wani dattijon mai gadi yana kallonsa,koda ajeebo ya fara komawa gida sai mai gadin nan ya rika bin shi a boye aboye har yaga in da ajeebo ya shiga Bayan isan Ajeebo gida da shigarsa daki ,ya zauna ya cigaba da zulumi da kuma nazarin wace mafita zai kara samu,wata zuciyar ta ce ya gudu ya bar garin ,haka dai ya kwana idonsa biyu cikin zulumi, a wata bangaren kuwa da gari ya waye sai yan unguwar sharada su ka tashi da sabon alamari na an samu gawar budurwa a unguwarsu nan dai aka samu wadanda su ka je su ka sanar da yan sanda. Ku Biyomu Shabun shafinmu danjin Irin wannan da ciga bansa Rayuwar Matasa a Yau Rayuwar Matasa a Yau
Posted on: Sat, 26 Oct 2013 10:25:30 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015