TALAUCI YA KARA KARUWA A MULKIN PDP NA SHEKARA 15 - Inji Bankin - TopicsExpress



          

TALAUCI YA KARA KARUWA A MULKIN PDP NA SHEKARA 15 - Inji Bankin Cigaban Afrika Bankin raya Cigaban Kasashen Afrika (African Development Bank) ya fitar da wani rahoto akan tattalin arzikin Nigeria a tsakanin shekarun (1999-2013). Bankin ya fitar da alkaluma kan talauci inda bankin yace ya karu da kashi 73.2 cikin 100 a kauyuka a yayin da a birane talaucin ya karu da kashi 61.8 cikin 100. Rahoton ya tabo karancin abinci da kuma cin abinci mai gina jiki, inda rahoton yace yawancin talakawa na cikin wannan yanayi na rashin abinci mai kyau. Rahoton ya kuma fitar da alkaluman rashin aikin yi inda yace duk shekara fiye da matasa Miliyan daya ke fara neman aiki kuma a cikin wannan adadi kadan ke samun abin yi. To amma kakakin Shugaban Kasa Mr. Reuben Abati yayi wa rahoto dirar mikiya inda yace zunzurutun karya ke cikin rahoton, kuma duniya ma ta sani tun da Jonathan ya zama Shugaba Kasa Nijeriya ke cikin walwala. To fa!! Via: Sakkwato Birnin Shehu
Posted on: Sun, 11 Aug 2013 11:14:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015