TASKAR FIM: Maja: Fim Din Da Aka Hada Ibro Da Osofia A Karo Na - TopicsExpress



          

TASKAR FIM: Maja: Fim Din Da Aka Hada Ibro Da Osofia A Karo Na Farko Tare Da Aliyu Ahmad A ranar Asabar din da ta gabata ne fitaccen kamfanin shirya finafinan Hausan nan mai suna Fhaidat Film Production ya kammala shirya sabon fim dinsa mai suna Maja. Idan ba a manta ba, kamfanin su suka shirya fim din barkwancin nan mai suna Oga Abuja, inda suka gayyato fitaccen jarumin barkwancin nan na finafinan Kudu, wato John Okafor, wanda aka fi sani da Mista Ibu, ya fito a fim Din Hausa a karo na farko. ya fita a fim din ne tare da shi da Rabilu Musa Ibro, Ali Nuhu, Saratu Gidado, Yakubu Muhammad da sauransu. A wannan karo ma kamfanin mallakar furodusa Abba Miko Yakasai, ya sake kafa tarihi a masana’antar finafinan Hausa, inda ya sake gayyato daya daga cikin finafinan na Kudu, wato Nkem Owoh, wanda aka fi sani da Osofia ko kuma Ukwa, inda aka hada shi da Rabilu Musa (Ibro) da sauran jaruman fim din Hausa da suka hada da Bello Mohammed Bello, Rabi’u Daushe, Yusuf Haruna (Baban Chinedu), Malam Dare da Sani Dan Gwari. Sai kuma a bangaren mata akwai A’isha Aliyu (Tsamiya), Hafsatu Sharada, Samira Saje, Fati Sammani da kuma sabuwar jarumar da aka gabatar da ita mai suna Rashido da kuma Saddika, wadda ake yi mata lakabi da a kori Jamila Nagudu. A yayin da ake kan hada shirin, wakilinmu ya nemi jin ta bakin Abba Ahmad Miko, Yakasai, wanda ya shirya fim din, yayin da kuma Usman Uzee ya dauki nauyin shirin, inda ya tambaye shi dalilin da ya sa yake hada jaruman Kudu da na Arewa, kasancewar fim din Oga Abuja ma na sa ne. Inda da farko ya fara da bayyana abin da sabon fim din na Maja ya kunsa, inda ya ce “shi dai wannan fim, za ka iya tunawa an yi sabuwar Jam’iyyar hadaka mai suna Maja, ka ga ita ita ma hadaka aka yi. To wannan Majar tawa ita ma an yi ta ne tsakanin Bahaushe da Inyamuri, wanda saboda wan¬nan gamayyar da aka yi ne ya aka kira fim din da suna Maja”. Sannan ya kara da cewa ba komai ne ke jawo hankalinsa ga hada jaruman Hausa da na Turanci a fim guda ba illa ganin an samu hadin kai a kasar da kuma kawo cigaba a harkar finafinan Hausa. Kuma hakan ya samo asali ne sakamakon wani matashi mai suna Usman Uzee, wanda tsohon mai kula da kwalliya ne a finafinan Kudu da yake taimakawa wajen gayyato musu jaruman na Kudu. Shi dai wannan fim Din, wanda Sadik Mafia ya bayar da umarni, labari ne da ya kunshi wata Bahaushiya (Hafsatu Sharada) da ta yi aure a kasar Inyamurai har ta haifi yaro daya (Osofia), daga baya da auren ya mutu ta dawo kasar Hausa ta sake yin wani aure ta haifi wani mai suna Sallau (Ibro), wanda ya addabi jama’ar garinsu. Inda sakamakon rashin kyautatawa jama’a da Sallau din ba ya yi ne, ya sa kanin mahaifiyarsa (Malam Dare) kawo wan Sallau (Osofia) daga kasar Kudu inda yake sana’ar tura baro domin ya zo ya ci arziki, kasancewar mahaifin Ibro ya rasu ya bar masa dukiya, amma kuma bai sani ba. Bayan zuwan Osofia ne, Sallau (Ibro) ya nuna cewa ba jininsa ba ne kasancewar ba ya jin hausa kuma al’adarsu ta sha bamban. Ya kamata masu sha’awar kallon finafinan Hausa su taryi wannan fim din da zaran ya shigo kasuwa domin ganin yadda za ta karke tsakanin Ibro da Osofia sakamakon yi masa awon gaba da kudin gado da ya yi bayan ya dawo daga kasar Kudu duk da cewa ba shi da iko a kudin, domin uwa suka hada, amma uba kowane da na sa. Kuma bayan Osofia ya yi nasarar guduwa da kudin, ya je birni ya sayi manyan gidajen alfarma ya na sheke ayarsa a ciki. Sannan kuma shiri ne da ya zo da sabon salo na barkwanci domin nishadantar da masu kallo. Idan za a iya tunawa Abba Miko Yakasai, shi ya shirya finafinai irin su Yaro Da Kudi, Guduma, daga bisani kuma ya yi finafinan gamayya da wani abokinsa mai kamfanin UK Entertaiment, inda suka yi finafinai irin su Garinmu Da Zafi, Maryam Diyana, Ajnabi. Daga bisani kuma ya koma yin finafinansa shi kadai a kamfaninsa na Faidat Films Production, inda suka yi finafinai irin su Kalisat, Jalaluddin, Waye Nawa?, Ni Da Matata, Habib, Oga Abuja, Azeema, Mai Farin Jini da kuma Maja, wanda aka kammala daukarsa a yanzu. Admin #followcome pin 2958459F
Posted on: Mon, 30 Sep 2013 10:57:11 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015