******** UWAR MIJI NA1******* ..........Tun sassafe nake tashi - TopicsExpress



          

******** UWAR MIJI NA1******* ..........Tun sassafe nake tashi nayi mata shara da wanke-wanke gashi lokacin sanyi ne ga tsohon ciki wata bakwai gashi miji na ya tafi cirani baya dawowa sai yayi wata hudu, abincin safe da rana da dare duk ni ce nakeyi sannan kuma idan na gama sai na wanke tukwanen gabadayan sannan zanje ta dan sanmini abincin wanda ko (mage) idan taci ba zai isheta ba. Uwar mijina irin matan nan ne, mara sa tausayi ko kadan bata tausayan gani da tsohon ciki amma hakan bai hana ta ta azabtar dani ba. Daka daka dayin surfe da debo ruwa a rijiya da nukan dutse duk ni ce nake yi kamar an kawo mata baiwa. (maid). Sannan ga kannan mikina har biyar gandara-handaran samari da kuma yan mata biyu duk babu mai kulani don har dukana suke suna cewa yayana ya aura me bakin kashi tunda ya aureni wai ya daina yi musu alherin dayake musu a da kapin yayi aure wanda har da uwar mijin nawa ita ma hakan take fada. Yau ma kamar kullum yadda na saba na dora girkin abincin (sanwa) rana ne, me bin mijina ya shigo yake tambaya ta ina abincin sa? Sai nake fada masa ban gama ba amma dan Allah yayi hakuri ina saukewa zai kawo masa har dakinsa cikin jan tsaki mtsssswww yayi mini sannan yasa hannuns mai kamar tabarar ya dungurar dani a gaban murhum wanda saura kadan hannuna ya fada kan garwashin wuta, amma Allah ya kiyaye ni ban ji ko kwarzane ba ballanta na ciwo kuma akan idon ta, uwar miji na akayi mini hakan, amma ko kanzil bata ce ba. Cikin shesshekakar kuka na na tashi na gyara zamana, sannan na iza wutar girkin hawaye ya cika mini ido nayi baki na rame, kullum cikin zullumini nake, a ce nayi ba dai dai ba. A cikin kannen mijin nawa akwai wadda jinini ya hadu da ita kuma ita kadai ce take tausaya mini, wani lokacin idan uwar mijin nawa ta sanya ni wanki tare muke yi wanda sai da akayi mata gargadin kar ta kara tayani idan ba haka ba kuwa jikinta zai gaya mata. Bazan taba mantawa ba watarana ana wani masifaffen sanyi da sassafe naji an kwara mini ruwan daya kwana cikin randa. Cikin firgici na tashi a lokacin ma barci nake a dakina, sai ji nayi tace dani tashi shegiyaa me bakin kashi wancan kayan wanki dakika bari uban ki ne zaiyi miki? Eyee ke nake tambaya??? Kinyi shiru??? Cikin marairai cewa nace da ita #INNA wallahi bana jin dadin jikina kuma mura ta kamani gashi babu maganin da sha, to ubanki ne ya bani kudin maganin da zan sai miki? Tashi kije ki wanke mini kayana da wuri in ba haka ba kuwa zaki gayawa yan garinku... Cikin bakin ciki da jimamin abinda yasa na auri dan ta nake ina tunanin alqawarin rayuwar da mijina AHMAD yayi mini. Ni AISHATU ina zan sa kai na??????? Ku biyo ni muji a inda zata sa kan nata....... Marubuci dan gawuna, Mawallafi #M.Adam
Posted on: Tue, 03 Dec 2013 22:52:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015