WANI MUTUM A CIKIN JIRGIN SAMA Abin mamaki baya karewa. Wata rana - TopicsExpress



          

WANI MUTUM A CIKIN JIRGIN SAMA Abin mamaki baya karewa. Wata rana ne wani MUTUM ya biya kudinsa najirgi Zai yi tafiya mai nisa. Shigarsa cikin jirgi ke da wuya sai su kayi ido hudu (4) da wani farar fata {bature}. Sai mutumin nan yayi murna aransa yake cewa yau Allah zai ciyarmu abincin turawa. Yake cewa ai duk abinda bature yaci shima shi zai ci. Da fara tafiyarsu da mintuna kadan sai ga kuku (mai dafa abinci) sai ya cewa bature {what do you want?} [me kake bukata?] sai yaanswer masa dacewa{nothing}[ba komai]. Sai aka zo kan mutumin shima sai yace {nothing} al-halin shi bature ya cika cikinsa daabinci shi kuwa mutumin yana jiran na jirgi. Zuwan kuku 3 amma duk abinda bature ya fada shi mutumin yake maimaitawa, wai a zatonsa {nothing} abinci ne mai wuyar dahuwa. Da dai yaga abinci bai karaso ba sai yafada dakarfi yake cewa 'IDAN BABU NOTHING DIN KAWO MIN KO SHINKAFA DA MIYA CE KO WAKE DA SHINKAFA YUNWA TA DAMENI.
Posted on: Mon, 01 Jul 2013 11:07:31 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015