WANNAN TA HAUSAWA CE - KARIN MAGANAN HAUSAWA 1.Abin rabone - TopicsExpress



          

WANNAN TA HAUSAWA CE - KARIN MAGANAN HAUSAWA 1.Abin rabone auren mace da ciki. 2.Duk inda jirgi yaje idan akai hakuri kunkuru ma zaije saidai yadade bai jeba. 3.Daga uhm sai uhm wai uwar gulma tayi cikin shege. 4.Ina ruwan wani da wani wai mahaukaci yayi bako. 5.yau da gobe mai sa amari Suruka. 6.Sara da sassaka baya hana gamji tofo 7.Mai hankali shi yake gane dingishin kwado......! 8.Mai rabon ganin badi ko ana dakawa a turmi.... 9.Mai hankali shi yake gane Baccin makaho... 10.WANDA YA GANI shiya ji kunya KALLON FITSARIN MAKAHO 11.Da zaman banza gara aikin kishiya 12.Allah kadai yasan karatun kurma, 13.RUWA a chokali ya ishi mai hankali wanka,,,,. 14.ko yaushe kare ya samu daman mike kafa 15Abu yayi dai dai ankama ango da uwar amarya 16.Gani yakori ji.... 17.Albarkacin kaza gadan gare yakansha ruwan kasko... 18.Da zaman banza gwamma aikin uwar kishiya. 19 gobara da kogi maganin su Allah . 20 Da muguwar Rawa gwamma kin tashi . 21 Kowa ya Raina tsaiwar wata, to ya hau ya gyara.
Posted on: Wed, 06 Nov 2013 20:33:53 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015