WASIKAR MAAIKI SAW Wannan hoton ainihin wasikar da Manzon Allah - TopicsExpress



          

WASIKAR MAAIKI SAW Wannan hoton ainihin wasikar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi wa Sallam ya aikawa Sarkin Rum Hiraqalu (Hercules) a farkon annabta ce, yana kiransa zuwa ga musulunci. Allahu Akbar! Allah ka tashe mu a tutar maaiki SAW da duk wanda yace ameen. KARIN BAYANI lokacin da Annabi (s.a.w) ya aika wasika zuwaga sarkin rum na wannan l0kacin maisuna hirKal sai aka iske sarkin makka abu sufiyanu yaje garin hutawa (lokacin kuwa sarkin makka bai ko musulunta ba) da sarkin rum ya karanta wasikar sai yasa aka kira masa abu sufiyanu ya tambayeshi daga wane tsatso muhammdun ya fito? Abu sufiyanu yace yafito ne daga zuria tsarkakakkia ta larabawa hirkal yace duk cikin zuri,arsu wani ya ta6a cewa shi annabin Allah ne? Abu sufiyanu yace Aa ba wanda ya ta6a cewa sai shi kadai sarkin rum yace to mabiyansa karuwa suke ko raguwa? abu sufiyanu yace karuwa sukeyi kwarai kullum sarkin rum yace mafi yawan mabiyansa daga masu arziki suke ko matalauta ? Abu sufiyanu yace daga matalauta sarkin rum yace imaninsu ga sab0n addinin nan mai karfi ne ko kuwa suna dai biye dashi ne? Abu sufiyanu yace imaninsu mai karfi ne kwarai da gaske sarkin rum yace muhammadu ya ta6a fadar wata magana ta karya kafin yakawo ga cewa shi annabin Allah ne? Abu sufiyanu yace karya kam bata ta6a fita daga bakinsa ba sarkin rum yasake cewa an ta6a kulla aminchi dashi ya karya? Abu sufiyanu yace har abada sarkin rum yace me yake koyawa jama,a ? Abu sufiyanu yace wai a bautawa Allah shi kadai a zauna zama nagari kuma a taimaki makwafta da dangi wannan hira tana nan rubuce cikin bukhari.
Posted on: Thu, 04 Dec 2014 13:17:16 +0000

Trending Topics



iv class="stbody" style="min-height:30px;">
You really want to start successful in network marketing !! YES
FALTAM 12 HORAS PRAZO FINAL, ACABOU DE SAIR NA MÍDIA, EXTRA

Recently Viewed Topics




© 2015