WATA BAZAWARA TA ZAMA ABIN TSOROgb WAZAI AURETA ??? Wani mutum ne - TopicsExpress



          

WATA BAZAWARA TA ZAMA ABIN TSOROgb WAZAI AURETA ??? Wani mutum ne ya auri wata bazawara, ranar tarewa ya shiga dakinta da dare sai ya iske ta tanata kuka, ga huluna uku a gabanta amma duk ciki ba irin na kan sa Sai mijin Ya tambayeta: “Ko lafiya kike ta kuka haka, maimakon murna?” Shi ne ita kuma ta amsa masa da cewa: “Wannan hular ta farko, ta mijina ce na fari, kwananmu uku da aure ya mutu. Hula ta biyu, ita ma mijina na biyu ke da ita, ya mutu ne kwanaki uku da daura aurenmu. Hula ta uku, mijina na uku ne ke da ita, kwananmu biyu da aure ya mutu. Shi ya sa nake kuka, tunanin cewa ga shi na yi sabon auren mutum na hudu ko…” Kafin ma ta ida batun, sai ya aje hularsa gabanta ya ce mata: “Ga hulata nan, in za ki ba da labari, sai ki ce ta mijinki ce na hudu, wanda ya gudu a ranar farko da daura aure!” Hahaha
Posted on: Mon, 26 Aug 2013 05:36:48 +0000

Trending Topics




© 2015