Wani Mutum Ya Rika Lallabar Matar Wani Limami Yana Son Yayi - TopicsExpress



          

Wani Mutum Ya Rika Lallabar Matar Wani Limami Yana Son Yayi Fasikanci Da Ita, Sai Matar Ta Sanar Da Mijinta, Sai Mijin Nata Yace Mata, Ta Umarci Wannan Mutum Da Yayi Sallah a Cikin Jami Har Na Tsawon Kwanaki Arbain. Sai Wannan Mata ta Fadi Ma Wannan Mutum Cewa: Idan Yana So Ta Biya Mashi Bukatar Shi, To Yayi Sallah a Bayan Mijinta Har Tsawon Kwana Arbain, Idan Yayi Hakan Zai Samu Abinda Yake Nema a Wajenta. Wannan Mutum Yayi Farin Ciki Sosai, Kullum Salla Bata Wuce Shi, Kuma a Bayan Mijin Wannan Mata Da Yake So Ya Nema. Hakan Kuwa Yayi Da Kwana Arbain Suka Cika, Matar Nan Taji Shiru Mutumin Nan Bai Tuntube ta Ba, Sai Ita Ta Tuntube Shi, Sai Yace Mata Wallahi Ya Tuba Ga ALLAH. Sai Ta Bawa Mijinta Labari, Sai Mijinta Yace:ALLAH(Maigirma da daukaka) Ya Fadi Gaskiya Da Fadar ShiHAKIKA SALLAH TANA HANA ALFASHA DA ABIN KI. Allah yasa mudace.....
Posted on: Sun, 03 Nov 2013 19:06:18 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015