Wani dan siyasa mai suna Alhaji Kabir Buraza unguwar Yarima ya - TopicsExpress



          

Wani dan siyasa mai suna Alhaji Kabir Buraza unguwar Yarima ya maka dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiyya, Sheikh Umar Abubakar a gaban kotun shari’ar Musulunci ta daya da ke Kofar Soro bisa wasu alkawurra da dan majalisar ya dauka zai yi masa bayan an samu nasara wanda har yanzu ya kasa biya masa su. Alkawurra da aka yi masa sun hada da kujerar Makkah, bada jari, zuwa Kasashen Turai, gina masa gida da kuma saya masa motar hawa wanda har yanzu ba’a yi masa ko guda ba. A zaman kotun wanda lauyan dan majalisar, IB Ibrahim ya wakilci wanda ake kara ya bayyana wa kotu cewa, a cikin takardar rantsuwa ya ce Kabir ya shigar da karar ce domin ya bata wa wannan dan majalisar suna. Lauyan ya ce, dan majalisar bai taba daukar masa wani alk-awari a maimako ma mai karar ya yi haka ne don kawai ya bata su¬nan dan majalisar da kuma ganin ya zubar da kimar sa a idon duniya, kuma babu wani alkawri da ya taba dauka, saboda a matsayin shi na Musulmi ya san daraja da mutunta alkawari da kuma illar rashin cika shi. Lauya Ibrahim ya shaida wa kotun cewa, dan majalisar ya taba ba mai karar Naira dubu dari biyu lokacin da zai aurar da diyarsa kuma ya taba bashi mashin da dubu dari biyu. Muna bayanin irin kyautatawar da yake wa alumma musamman na mazabar shi ta Kat¬sina ta tsakiya. Alqali Kabir Safana ya tambayi wanda ya shigar da karar, Kabir Brother ko yana da wasu shaidu da zai gabatar kotu na tab¬batar da kotu, wanda suka san anyi wannan alkawari, Kabir ya ce yana da shaidu kamar haka akwai Hadiza wadda ita ce uwargidan Sheikh Umar , Dan Kankiya, Isyaku ‘Yandoma, Abbati Barmo, Abu VC, Jantili Kafinta da kuma Bishir Kabir Murja. Tuni dai Kotu ta bada umurni a rubuta wa wadannan mutane sammace domin halartar zuwa bada shaida a zama na gaba. Alkali Kabir Safana ya dage sauraron karar zuwa ranar 24/09/2012 domin fara sauraren shaidu.
Posted on: Fri, 04 Oct 2013 23:34:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015