ZUCIYA TA GARI ... DUKIYA, MULKI, - TopicsExpress



          

ZUCIYA TA GARI ... DUKIYA, MULKI, ILIMI. …¨…¨¨…¨…¨¨…¨…¨¨…¨… DUKIYA: Idan ta taru tayi yawa babu abin da take karawa mutum illa girman kai da nuna isa da ganin babu wanda ya isa, don haka mu kiyayi dukiya. MULKI: Idan mulki ya zama mai karfi ya tumbatsa, babu abin da yake karawa mutum illa girman dai da alfahari, domin abin da ka umarta shi za’ayi. Mu kiyayi mulki. ILIMI: Idan ilimi a tumbatsa ya mamaye mutum babu abin da yake karawa sai qanqan da kai da tawali’u da ganin girman Ubangiji. Domin Shi Ubangiji kana kara sanin sa, kana kara ganin girman sa da ganin girman halittar sa. Sabanin wadan can abubuwa guda biyu da suke haifar da halayen da Ubangiji baya so. Shi yasa yake wajibi gare mu da mu nemi ilimin sanin Allah, domin idan muka san Allah dukiyar mu da mulkin mu bazai haifar mana da girman kai da alfahari ba sai dai ya haifar mana da tsoron Allah da kumaqanqan da kai. Allah ya bamu ilimi mai albarka Da Amfani. Ameen
Posted on: Mon, 05 Aug 2013 15:51:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015