daga saifullahi M Kabir Cigaban......... HADISIN SALMANUL - TopicsExpress



          

daga saifullahi M Kabir Cigaban......... HADISIN SALMANUL FARISI AKAN MUTUWA DA ABIN DA TA KUNSA »»»»»¤¤¤•••| (Kashi Na 2)|•••¤¤¤«««««« Karantawar Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) A lokacin ina kallo iyalaina suka bazama suna ta kuka, labari ya isa zuwa ga yanuwa na da makotana, sai nace dashi, Kai kuma kaine wane wanda alamarinsa ya shagaltar dani ga barin Iyalina da dukiya da yayana, gashi kuma na firgita da ganinka? Sai yace nine Malaikan Mutuwa, nazo na dauki ranka ne, kuma na cireka daga gidan duniya zuwa gidan lahira, domin zamanka na duniya ya kare, mutuwarka tazo. Muna cikin haka nan, yana magana da ni, sai wasu su biyu suka zo min, suna da kyan kama, kyansu yafi duk irin kyan da na taba gani a cikin halittan Allah. Sai dayansu ya zauna a damana daya ya zauna a haguna. Sukace min: Sallama a gareka ya kai bawan Allah da rahamarsa da albarkarsa, Munzo maka da littafinka ne, karba kaga abin da yake ciki. Sai nace musu; Ku kuma kune wane Allah ya rahamsheku, kuma wane littafi ne kuka bani na duba na karanta. Sukace Muna malaikun nan 2 da muke tare da kai a nan gidan duniya. Muna rubuta abin da ke gareka da abin da ke kanka, to wannan Littafin kane, Yayin da na duba littafin kyawawan ayyuka na, sai naga abin da ke cikinsa, sai nai murna mai tsanani, naji dadi. Da na duba kuma bangaren littafin munanan ayyukana, wanda yake hannun Atidu, sai abin ya bakanta min rai ya sakani kuka. Su biyun, sai suka ce min, Albishirinka, kana tare da alkairi Sai kuma wani mutum ya gabato ya fizgi raina, kowane fizga ina jin tsananinsa kamar tsayawan sama zuwa kasa, bai gushe ba yana ta fizgan ran, kai kace ya dora min duwatsun duniya ne. Ya shiga fizgan raina, tun daga yatsuna, kafafuna, yana fitarwa. A lokacin iyalina suna ta kururuwa. Komai ake aikatawa ina iya fahimta. Yayin da kukansu da kururuwansu ya tsananta, suna tausayi na a halin da suka ganni. Sai shi Malaikan da ya ke daukan rai ya dube su a fusace, yana cewa: Kuna kukan mene? Ai bamu zalunce shi ba, bamuyi masa shisshigi ba, kuna ta kururuwa kuna kuka, ai daku da mu duk bayin Allah ne, da dayanku ne akace yayi mana abin da muke muku, shima abinda zai mana kenan, bamu dauki ransa ba sai da muddarsa ya kare. Zamu kuma kai shi ga Sarki mai girma, kuma shi mai iko ne kan komai. Ko ku daure ko kuyi kururuwa, in kun daure shi yafi muku alkairi, dan zaku sami lada, in kuma kunyi kururuwa zakuyi laifi. Kuma ai na dinga dawowa kenan (inji malaikan mutuwa), akwai iyaye da mata, da yara da jikoki suna nan tafe. Sannan ya juya da ruhina, ya dauki ruhin yana tare da shi, sannan sai wani Malaika kuma yazo ya karba daga hannunsa, ya sata a wani tufa kore na hariri, sannan ya dagata sama, yaje ya sanyata gaba ga Allah Mai Girma da Daukaka. Yayin da ruhina yakai gaba ga Ubangijina (SWT) sai Allah ya tambayeta dangane da karami da babba. Ya tambayeta dangane da Sallah, da Azumi a watan Ramadan, da Hajjin dakin Allah, da karatun al-Kurani, da Zakka da Sadakoki, da sauran lokuta da raneku, da daan iyaye, ya tamabayeni dangane da kashe rai ba tare da hakki ba, da riba, da cin dukiyar maraya, da zina da alfasha iri daban daban, da zaluntan bayi, har an tambayeni dangane da tsayuwar dare (Tahajjud) a yayin da mutane ke bacci. Bayan duk Allah (T) ya gama tambayoyin, sannan sai aka dawo da raina zuwa kasa, to a yayin nan ne mai wanka yazo, ya shiga tube min riga yana wanke ni, sai na kirashi ina cewa: Na gama ka da Allah ya kai wannan bawa, kaji tausayin jikina mai rauni, duk lokacin da ka juyani sai naji zafi. Da ace mai wankan nan yaji maganar da nakeyi da shima ya mutu. Sannan ya zuba min ruwa yai min wanka uku. Sai ya saka min likkafani tufafi uku, yai min halodi shine guzurin da na fita dashi izuwa lahira. Sannan ya cire zobene a hannuna na dama ya mikama babban Da na, yace: Ajarakallahu fi Abika wa ahasana lakal ajara wal aza, sannan ya nannadeni a likkafani, ya kira iyalina da makwaftana, yace kozo ai bankwana. Sukazo suna bankwana da ni, yayin da aka gama bankwana da ni, aka daukeni a makara na katako, suka daukeni a kafadu 4, ruhina na tsakanin fuskana da likkafani na, tana tsaye a makarana, tana cewa: Ya Iyalaina! Ya Yayana! Kar duniya fa tai wasa da ku kamar yadda tayi dani. Gashinan na tattara muku halas da ba halas ba, na jin dadi da lafiya, to kuji tsoro dangane da abin da na bar muku. Ban gushe ba ina haka nan, har suka sanyani domin Sallah, sukai min Sallah, bayan da suka gama min Sallah aka daukeni zuwa ga Kabarina aka sakani a ciki, sai aka daga ruhina tsakanin kafaduna da fuskana, aka kusantar dani a kabari aka sakani a rami, naga firgici babba. Zanci gaba Insha
Posted on: Thu, 28 Nov 2013 20:28:29 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015