**fillo kenan** Wani bafulatani ne koda yaushe sai yaji ana yiwa - TopicsExpress



          

**fillo kenan** Wani bafulatani ne koda yaushe sai yaji ana yiwa agogo kirari ana cewa agogo sarkin aiki sai ran nan yace sai yaga iyakar aikin agogo yaje ya siyar da saniyarshi guda 1 yaje kasuwa yace azabo mai agogo wanda yafi kowane girma aka bashi da yaxo gida yacewa matarsa adama fura zaije da agogo gonarsa domin ya masa aiki kawai ya dauki fura tare da agogo sai gona yana ajewa kawai ya dawo gida ya sami guri yayi kwanciyarsa, kawai sai ga wani yaxo wucewa ta gonar yunwa ta koro shi kawai sai yaga fura da nono kawai ya kama ya shanye ya tafiyarsa chan rana tayi sanyi saiga gogan naku yaxo gona yana xuwa sai yaga agogonsa na nan inda ya ajiye amma kuma an shanye fura sai ya dawo gida yana fadawa matarsa ashe agogo ba sarkin aiki bane fura kawai ya iya sha...hmmmm
Posted on: Wed, 03 Jul 2013 12:02:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015