sabuwar PDP Ta Zargi Bamanga Da Taimaka Wa APGA A Zaben Anambra - TopicsExpress



          

sabuwar PDP Ta Zargi Bamanga Da Taimaka Wa APGA A Zaben Anambra Sabuwar PDP, ta zargi shugaban jamiyyar PDP na kasa, Alhaji Bamanga Tukur da sauran shugabannin jamiyyar da taimaka wa jamiyyar APGA a zaben Anambra, saboda da a zaben 2015, a yi ban gishiri na ba ka manta. Bangaren na Kawu Baraje, ya ce kafin su yi wannan zargi sai da suka tabbatar da gaskiyar hakan, PDPn ta yi haka ne don a zaben 2015, APGA ta tsaida Goodluck Jonathan a matsayin dan takararta. Saboda haka jamiyyar ta goyi da bayan dan takarar APGA, Mr. Willie Obiano, a lokacin zaben da aka yi satin da ya gabata. Wannan zargi na kunshe ne cikin wani jawabi da sakataren yada labaran sabuwar PDP, Chukwuemeka Eze ya sanya wa hannu, inda ya nemi kwamitin ladaftarwa na Umar Dikko ya rufe ido ya gayyato Bamanga don a ladaftar da shi. Sai dai Bamangan ya yi watsi da zargin, inda ya ce masu yin sa ba su da nutsuwa, saboda haka ya kamata yan PDP da sauran yan Nijeriya su daina laakari da duk wani zargi da zai fito daga wurinsu.
Posted on: Fri, 22 Nov 2013 08:50:13 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015