A KASARNAN BA DALIBAI SAM Nasan dayawa mutane musamman yan boko za - TopicsExpress



          

A KASARNAN BA DALIBAI SAM Nasan dayawa mutane musamman yan boko za suyi mamakin fadin wannan magana tawa, emana babu dalibai a kasarnan dominda da akwai da babu wani mai mulki da har zaiyi wasa da rayuwarsu, maana ILIMINSU. A duk fadin duniya akanyi amfanida dalibai wajan cimma wasu bukatu koma wani sain daliban kan kwatarwa talakawa yanci ta hanyar yin fito na fito da duk wani tsari da baiyimusu ba. Idan ba mantaba a kasashe irinsu, German. England. Us. Turkey. Niger da Camaron kasashene da dalibai kan taka muhimmiyar rawa wajan kwato yanci ga yan kasa bare kuma nasu. Shin me yake damun daliban kasr nan ne? Anya karatun kuwa mukeyi? Dominda karatun mukeyi da babu wani da zai mana irin wannan cin zarafi ta hanyar hana malamanmu haqqinsu wanda sukuma suka shiga yajin aikin da ba wanda yasan karshan shi? Idan da kasar da mukaci gabane da tuni dalibanda ke kano sun hana shiga da fita a kanon, haka na kaduna, katsina, sokoto, Lagos da Pht duk mu hana kowa motsi ta hanyar hana kuwa shiga da fita, hatta Abuja har sai hukuma ta saurari kukanmu. Shin haka zamu zuba ido ana tafiya?
Posted on: Fri, 06 Sep 2013 21:41:53 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015