A kwai Hannun kasar Saudiyya game da rikicin kasashen Gabas ta - TopicsExpress



          

A kwai Hannun kasar Saudiyya game da rikicin kasashen Gabas ta tsakiya. A wata tattaunawa da ya yi da tashar talabijin din Fox New ta Amurka, ministan harkokin wajen kasar Saudiyya Yarima Sa’ud Faisal ya tabbatar da cewa kasar Saudiyya ta kashe makudan kudaden don sauya gwamnatocin yankin Gabas ta tsakiya. A cikin tattaunawar, Sa’ud Faisal ya tabbatar da cewa Saudiyyar ta kashe biliyoyin dalolin Amurka wajen kirkirowa da kuma yin tasiri cikin abubuwan da ke faruwa a kasashen larabawa musamman a kasar Masar. Har ila yau ministan harkokin wajen na Saudiyya ya ce kafin da kuma bayan yunkurin al’ummar Masar musamman bayan kifar da gwamnatin Muhammad Morsi, Saudiyyar ta ba wa wasu kungiyoyi masu tasirin gaske a kasar Masar din makudan kudaden duk dai da nufin yin tasiri kansu da kuma yunkurin al’umma da suke neman sauyi. Wannan bayani na Sa’ud Faisal dangane da kudaden da Saudiyya ta kashe wajen sayen kungiyoyi da mutane masu tasiri a kasar Masar da kuma rawar da kasar ta taka wajen kifar da gwamnatin Ikhwanul Muslimin karkashin jagorancin Muhammad Morsi ya zo ne a daidai lokacin da masana da majiyoyin yada labarai suke ta karin haske dangane da irin rawa da kuma kokarin da kasashen Saudiyya da Qatar suka yi wajen tabbatar da gwamnatocin kama-karya a yankin Gabas ta tsakiya da kuma hana hakikanin yunkurin neman sauyi na al’ummomin yankin samun nasara ko kuma idan ma sun yi nasarar to su sami hanyar da za su yi tasiri kansu. To sai dai kuma duk da wadannan makudan kudaden da Saudiyya ta kashe kuma take ci gaba da kashewa har ya zuwa yanzu bai haifar musu da hakikanin abin da suke so ba, mai yiyuwa hakan ne ma ya sanya Sa’ud Faisal din fadin cewa taimakon da suke ba wa Masar fa ba zai ci gaba har abada ba. Wanda hakan yana nuni da irin damuwar da Saudiyyan take ciki ne na rashin ganin tasiri na hakika na irin wannan aiki da a mafi yawan lokuta ya kan zama aikin baban giwa. Rahotanni da maganganun jami’an kasashen Siriya da Iraki, haka nan kuma a cewar masharhanta a kasashen Yemen da Tunusiya, tsawon shekaru biyun da suka gabata, Saudiyya ta kasance kanwa uwar gami cikin kururuta wutar fitinar da ke faruwa a kasashen larabawan. A cewar masanan bayan raunana matsayin Turkiyya cikin rikicin kasar Siriya da kuma boren da gwamnatin Turkiyan take fuskanta a cikin gida, haka nan kuma da sauyin mulkin da aka samu a kasar Qatar, bugu da kari kan irin nasarorin da gwamnatin Siriya take samu a kan ‘yan ta’addan da aka shigo da su kasar, daga dukkan alamu kasar Saudiyya, ta hannun shugaban cibiyar leken asirinta Bandar bn Sultan sannan kuma bisa goyon bayan Amurka, tana kokari ne wajen ganin ta juya yunkurin neman sauyi na al’ummar Gabas ta tsakiya don tabbatar da manufofin Amurka da haramtacciyar kasar Isra’ila. Masanan kasashen yammaci sun tabbatar da cewa a halin yanzu kasar Saudiyya ita ce babbar hanyar da ‘yan ta’adda da sauran masu dauke da makami da suke yakin gwamnatin Siriya suke samun makamai da kudaden da suke bukata wajen ci gaba da ayyukan ta’addancin da suke yi a kan al’ummar Siriya da nufin raunana gwamnati da al’ummar kasar wadanda suka zamanto karfen kafa ga haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma bakaken manufofinta a kan al’umma. Baya ga kasashen Masar da Siriya da Yemen da Tunusiya, har ila yau kasar Saudiyyan tana da hannu dumu-dumu cikin rikicin da ke faruwa a kasar Iraki na irin bama-baman da ‘yan ta’adda suke tayarwa a cikin kasar da ke ci gaba da zubar da jinin mutanen da ba su ci ba su sha ba. Hakan ne ma ya sanya jami’an kasar ciki kuwa har da firayi ministan Maliki fitowa fili da jan kunnen Saudiyyan kan hakan. Babbar manufofi kasar Saudiyya da wasu kasashen larabawa irin ta cikin abin da ke faruwa a kasar Irakin ita ce kifar da gwamnatin Nuri Al- Maliki ta kasar wacce ta ki mika musu kai da biya musu bukatun da suke so. A saboda ko shakka babu rikici da ayyukan ta’addancin da ke faruwa a kasashen Siriya da Iraki, wani sabon makirci ne na Amurka da ‘yan amshin shatanta irin su Saudiyya da nufin kawar da duk wata kasar da za ta zamanto musu karfen kafa wajen cimma bakaken manufofinsu.
Posted on: Mon, 09 Sep 2013 10:15:10 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015