A lokacin taron ranar Lahadi 11/08/2013 wanda akayi a gidan Alh - TopicsExpress



          

A lokacin taron ranar Lahadi 11/08/2013 wanda akayi a gidan Alh Namadi Inuwa dake unguwar G/Dutse, duk da ruwa da aka yammanta dashi a wannan rana amma wasu daga cikin iyayen mu sun samu halartar wannan taro. Ko da yake ba sharhin wancan taron na ke son yi ba a wannan lokaci, amma ina son yin sharhi ne akan wata magana ko na ce shawara da wani ya bayar lokacin da aka bashi damar magana. ga abun da ya ke cewa: "duk da cewa ba taba halarta taron nan ba a kuma taba gayyata ya ba sai yanzu bansan akan abunda ake taron nan ba da manufarsa da abun da aka sa a gaba. ina son na bamu shawara ko nasiha a dunkule wanda idan ka dauka tana da fadi ta dauki abubuwa da yawa, shine aji tsoron Allah. duk abun da za ayi ayishi domin Allah sai a samu nasararsa a kuma cimma buri. idan mutum goma suka taro akan wani aiki na alkhairi mutum uku suke yi domin Allah shauran bakwai suna yi ne dan wata manufa to ba za su tabba samun nasara ba, sai a bar wadancan mutum uku suyi ta wahala suna samun ladansu amma ba za su tabba samun nasara ko cimma burin abun da suka nufa ba. Haka kuma idan mutum goma suka taro akan wani aiki na alkhairi mutum bakwai suke yi domin Allah. mutum uku suna yi don wata manufar to Allah zai basu nasara akan abun da sukayi nufin aikatawa. Wannan ita ce sunnar Allah..." ya kamata ko wannen mu ya dubi wacen maganar ta wannan bawan Allah duba na tsanaki. ya kalli rayuwa da tarihin magabata nasarorin da suka samu da kishiyarsu a lokacin da sukayi tarayya wurin aikata wani abun alkhairi. Duk wanda yau aka ce ya daukaka a duniya ya na fadin cewa baban abun da ya kawo shi wannan matsayi shi ne imani. mu kuwa muslmi Allah ya sanar damu a cikin littafinsa mai girma wanda duk ya ji tsoransa ya yi aiki don shi za buda masa hanyoyin samun nasarori.
Posted on: Wed, 21 Aug 2013 22:42:13 +0000

Recently Viewed Topics




© 2015