AKODA YAUSHE KANA AMFANI DA COMPUTER/WAYA Akwai wadanda akoda - TopicsExpress



          

AKODA YAUSHE KANA AMFANI DA COMPUTER/WAYA Akwai wadanda akoda yaushe suna amfani da Computer ko wayar salula wajen tafiyar da harkokinsu kamar na kasuwanci kona office, wasu kuma wuni suke akan shafukan sada zumunta ko gajiya basayi balle tunanin lafiyarsu. Ya kamata mu rika dan hutawa, domin yana da amfani, yawan amfani da waya ko computer akoda yaushe yana haifar da matsala mai girma. Sannan yana canza yanayin mutum daga yadda yake zuwa wani yanayi na daban, kadan daga matsalolin da suke faruwa. 1. MATASALAR IDO/ZAFIN IDO Yawan kallon hasken screen na waya ko computer na haifar da zafin ido, wato kaji idonka kamar yaji ya shiga, wani lokacimma kaji jijiyoyin da suke jikin idonka kamar zasu fadi. Wani lokaci, mutum yakan tashi yana gani dun-dumi-dun-dumi, amma duk da haka wani yakan wuni yana yi, inda son samu ne karka wuce awa uku baka ajiye ka huta ba, amma sai mutum ya wuni yana kallon hasken screen, harma mutum yakan ce aina saba, ko kuma saboda ana cewa, ..wane mayan intanet ne kullum yana kai karka biye irin wadannan ka rika hutawa dadewa akai yana haifar da matsala kala-kala. *. Wanda yake kaiwa 3hrs duk rana, ganinsa yana raguwa da kashi 13% cikin dari. *. 4-6hrs aduk rana karfin idonka zai ragu da kashi 28% cikin dari, *. Wanda yake kaiwa 7-9hrs aduk rana ba tare da ya huta ba, karfin idonsaa yana raguwa da 26% *. Wanda yake kaiwa 10-12hrs aaduk rana karfin idonsa yana raguwa da 21% *. Wanda yake kaiwa 12hrs idonsa yana raguwa da kashi 12% Saimu kiyaye idonmu daga gaani gara-ra-gara-ra. 2. CIWON WUYA Wuyan mutumin da koda yaushe yaanaa kallon waya ko computer zai rika damunsa da ciwo saboda yawan sunkuyo da wuyansa yake yi. Zai rika damunsa wani lokaci zaiji kamar ya dau kaya mai nauyi. 3. CIWON KAFADA Sannan mutumin da yake amfani da waya ko computer koda yaushe, zai rika famaa da ciwon kafadunsa, saboda koda yaushe kana ta motsi da shi, wani lokaci kakanji, kamar ka fadi akansa wato duk yayi maka tsami. 4. BUSHEWAR IDO Yawan kallon hasken screen naa sa idon mutum ya bushe, wato ya rika juriya wajen zubaa ido, ta yadda zaka ga wanda bai saba ba, idonsa har hawaye zaka ga yanayi. Saboda ya zuba idon dayawa. 5. KASALA DA CIWON JIKI Wanda yake yawan amfani da waya ko computer, yakan ji duk jikinsa kamar anyi masa duka, lokaci daya ya kamata mutum ya rika hutawa, wani yana jin kirjinsa yana masa zafi, amma ya kasa dainawa, mu kula da lafiyarmu. YADDA ZAMU KARE IDONMU DAGA HASKE Kadan daga hanyoyin da zamu kare idon mu daga matsalar screen shi ne: 1. Goge screen akan lokaci, karka bar shi cikin datti, ko akwai wata kura akan screen naka, yanzu zata sa idonka ya fara hawaye, da ganin daya a biyu. 2. Ka rage hasken screen naka, duba da lokaci ko yanayi na wurin da kake aikin ko lokacin. 3. Ya kasance dakin da kake aikin ka ya kasance mai kyan kala, karya zama fari fata, karya zama baki ko ja, san samu ya zama ruwan madara, wanda bazaisa kaga daya a biyu ba, da zarar ka dago da kanka ba. 4. Ka kasance kana sa glass mai kyau a idonka yayin da kake aikinka. 5. Ka kasance da screen guard akan wayarka idan da ita kake amfani. 6. Ka rage Light sensor yayin da kake amfani da computer ko waya.
Posted on: Tue, 05 Nov 2013 10:01:03 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015