ALLAH YA BASHI MASIFAFFIYAR MATA!!! Via: ZAUREN FIQHU Assalamu - TopicsExpress



          

ALLAH YA BASHI MASIFAFFIYAR MATA!!! Via: ZAUREN FIQHU Assalamu alaikum dan Allah mallam abani shawara.mallam ina da mata biyu amma wallahi uwargidan ba taso azauna lafiya musammam idan ina dakin Amarya har labe takeyi mana.(Domin taji abinda mukeyi) in wani abu ya hadomu da ita sai ta dinga cemin: KANA RABA DARE KUNA HIRA (JIMAI DA AMARYA) Mallam maganganu marasa dadi kamar ba mijinta ba. kuma wallahi Mallam bata da wata magana sai ta batanci akaina KO AGABAN WAYE. maana agaban kawayenta, yan uwanta, kai harma da yan uwana. Mallam dan Allah aban shawara. (DAGA DALIBINKA) AMSA ****** Gaskiya Malam ka hadu da Jarrabawa ko imtihani daga Ubangiji. Shi kuwa jarrabawa baa cinsa sai da hakuri da addua da juriya. Abisa yanayi irin na Matanmu na yanzu, su araayinsu, INDAI KA MUSU KISHIYA, TO KA RIGA KA AIKATA MUSU BABBAN LAIFIN DA BABU IRINSA AWAJENSU. Sun manta cewar Umurnin Allah ne. Don haka dole ka fahimci wannan. Kai amatsayin mai laifi kake awajenta. Sai dai kuma akokarin ganin laifin naka harma ta Qetare iyaka. Tana yin tereren sirrukanka tana yi maka cin mutunci. Wannan abinda take yi ya fitar da ita daga sahun mataye nagari. Allah (SWT) yana cewa: SALIHAN MATA SUNE MASU KAMUN KAI, MASU KIYAYE SIRRI Sannan kuma wannan labewar da take yi shima yana daga cikin CIN AMANA. Domin Allah ya hana binciken Kwakwaf. Amma ka san su mata bincike ya nuna cewar 80% (kashi tamanin) na kishinsu, AKAN JIMAIN DA ZAKAYI DA KISHIYARSU NE. Don hakane wasu matan suke labewa domin suji, su tabbatar. Sannan ranar da kake dakinsu kuma maimakon su ma su yi maka kwalliya suja hankalinka, AA sai dai masifa da balaI da rashin kunya. Basu jin haushin abincin da kishiya zata ci, ko suturar da zata sa ayawancin lokuta. Don haka sai dai ka Qara hakuri, kuma ka daure. Musamman ma idan kuna da yara, kayi hakuri domin Allah kuma saboda yayanka su taso cikin kwanciyar hankali. Amma babu laifi ka sanar ma iyayenta komai da komai. Kar ka rage ko daya. Watakil zasu fahimci cewar tana da laifi, suyi mata fada. Watakil idan anyi hakan zaka samu sauki. Idan kuma duk ka riga ka jarraba wadannan hanyoyin amma abin yaki sauyawa, me zai hana ka turata gidansu ta danyi 3 weeks?? Kar ka saketa. Kawai hutu zaka bata na yan wasu kwanaki.... Idan ta huta watakil zata gane kurenta. Allah ya sawwake. Yan uwa Maza da Mata ku bashi shawara.
Posted on: Wed, 30 Oct 2013 06:24:55 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015