Ammar Bin Yasir Gabatarwar Mujtaba Adam: “Baya ga - TopicsExpress



          

Ammar Bin Yasir Gabatarwar Mujtaba Adam: “Baya ga kasantuwar Ammar Bin Yasir sahabin Ma’aikin Allah wanda ya bada imani da shi, tun a shekarun farko na bayyanar Musulunci, yana kuma daya daga cikin wadanda su ka taka gagaruwar rawa ta fuskar tsarin zamantakewar al’ummar musulmi. Wannan, ya maida shi zama daya daga cikin wadanda manazarta masu mahanga daban-daban su ka maida hankali wajen yin bincike akan rayuwarsa. Wannan bayanin da zai zo a kasa, daya ne daga cikin nazarin da aka gudanar akan Ammar. Wanda ya yi shi, mai suna Farfesa Aliyul-Wardi, malamin ilimin zamantakewa ne (Sociology) na kasar Iraki. Ya kuwa maida hankali ne wajen yi wa rayuwar Ammar fida ta fuskar ilimin zamantakewa ba ta fuskar akida ba. Kuma saboda kasantuwar nazarin yana da tsawo, sannan kuma da la’akari da gandar karatu da mafi yawancin Hausawa su ke da shi, an karkatsa shi da kuma bai wa bangarorinsa jigo-jigo domin jan hankalinsu su daure su karanta. Sai dai shakka babu da akwai izina mai yawa ga rayuwar wannan bawan Allah, ga wanda ya ke son daukar izina, sannan kuma da sharhi ba irin wanda aka saba da shi ba akan yadda al’ummar musulmi ta kasance a daidai lokacin da Ammar din ya ke rayuwa. Da fatan za a ji dadin karatu da kuma daukar izina. Nuna wa Ammar Wariyar Launin Fata: Idan mu ka yi nazarin rikicin da ya barke a tsakanin Kuraishawa da talakawa a lokacin Usman, to za mu ga cewa Ammar Bin Yassir ya taka rawa mafi muhimmanci aciki. Watakila rawar da Ammar ya taka a lokacin wannan rikicin ta dara ta kowane mutum ta wata fuska. Ya dace mu fadi cewa ya fi Abu Zar tsanani a cikin gwagwarmayarsa da Usman haka nan kuma ya fi shi yin magana gaba-gadi da kuma yin fito na fito. Ya kuwa fuskanci wahala mai tsanani sanadiyyar hakan. Zubin zatin Amma ya banbanta da na Abu Zar ta fuskoki da dama. Abu Zar balaraben kauye ne da ya fito daga kabilar da ta ke rayuwa a tsakiyar sahara- ita ce kabilar Gaffar. Shi kuwa Ammar ‘yantaccen bawan birni ne wanda aka haife shi a makka ya kuma yi rayuwa mai tsawo a matsayin bawa. Launin fatar Ammar wankan tarwada ne ko kuma wanda ya yi kama da baki. Ya gaji wannan launin fatar tashi ce daga mahaifiyarsa wacce ‘yar Habasha ce. Wani abu da ya dace a yi ishara da shi anan shi ne cewa a wancan lokacin larabawa suna wulakanta wanda launinsa ya ke wankan tarwada ko baki. Farin launi yana daga cikin alamar daukaka a wurinsu. Idan su ka yabi mutum sai su ce masa: “Mai farin hannu” Idan kuma suna son su yi ishara da wasu mutane da su ke yabawa sai su fadi cewa: “Mu nufi wurin fararen mutane.” Watakila kin jinin bauta da larabawa su ke yi ne ya sa sami wannan tunanin. Bakin launi shi ne launin mafi yawancin bayi. Har a wannan lokacin kabilun larabawan kauye a Iraki suna kaskantar da wanda ya fito daga tsatson bayi. Wanda duk ya zagi wani ta hanyar dangata masa bauta to ya cancanci a yi masa ukuba. Ammar Bin Yassir ya rayu cikin wannan matsalar. Kuraishawa sun rika aibata Ammar da cewa shi: “ Bakin bawa” ne. A lokacin da Marwan ya zuga Usman da ya kashe shi ya aibata shi da cewa: “ Wannan bakin bawan ne ya tunzura mutane akanka. Idan ka kashe shi to ka yi maganinsa. Sai su ka yi masa duka har sai da ya suma.” ( Abqariyyatul-Imam: Abbas Aqqad.) Khalid Bin Walid ya kai karar Ammar a wurin annabi sai ya fada masa: “Wannan bakin bawan.” ( Ammar Bin Yassir: Abdullah al-Subaiti.) A lokacin yakin Siffain Mu’awiyya ya yi magana akansa yana cewa: “ Larabawa sun halaka idan su ka biyewa bakin bawa.” ( Littafin da ya gabata.) Ammar da ya ke kare kansa a gaban Kuraishawa a wannan rana ya fadi cewa: “ Mutum mai girma shi ne wanda Allah ya girmama shi. Na kasance kaskantacce sai Allah ya daukaka ni. Na kasance bawa sai Allah ya ‘yantar da ni. Na kasance mai rauni sai Allah ya karfafani. Na kasance talaka sai Allah ya wadata ni.” Ammar ya yi wannan magana ne a lokacin da Amru Bin As ya aibata shi da bakin launin fatar mahaifiyarsa. ( Littafin da ya gabata.) Dalilan da Ammar ya kafa dalilai ne irin na mutane karabiti wadanda suka taka matakalan kaiwa ga daukaka da kansu. “Ya’yan mutane masu jan wuya da matsayi ba su fahimtar wannan irin dalilin. Masu jan wuya suna daukar matsayin da su ke da shi abin fankama kuma suna jin cewa shi ne komai. Ba su daukar cewa gina kai da mutum zai yi ya fi dangatakarsa ta jini da matsayi, kima ba. Ammar yana hake da Kuraishawan da su ka azabtar da shi kuma su ke yi masa girman kai da kuma aibata shi da mahaifiyarsa. Yana daukar mahaifiyarsa da ta ke shahidiyar farko a Musulunci a matsayin tushen alfahari a gare shi. Su kuwa kuraishawa suna daukr ta a matsayin tushen kaskanci a gare shi. Yana kiran kansa “Dan shahidiya” su kuma suna kiransa “Dan Bakar mace” Matsalar biladama ita ce kowanensu yana yi wa lamurra matsayi ne bisa ma’auni nashi na kanshi. Kowane daga cikinsu yana kallon abubuwan bisa yadda ya ke ganin da ya dace da shi, ya kuma ki jinin wani abu bisa sonsa. An yi cacar baki tsakanin Ammar da Abdullahi Ibn Abi Sarh a lokacin yi wa Usman Mubaya’a. Ibn Abi Sarh yana goyon bayan Usman sai Abu Zar ya fada masa cewa: “Yaushe ka zama mai yi wa musulmi nasiha?” Sai wani mai goyon bayan Banu Umayya ya maida masa martani da cewa: “ Ka wuce iyakarka ya kai Dan Sumayya. Ina ruwanka da yadda Kuraishawa za su zabi sarkinsu? “ Suna aibata Ammar da mahaifiyarsa. Zagi mafi muni a wurin balarabe shi ne a danganta mutum da mahaifiyarsa. Suna kiransa “Dan Sumayya.” Suna cewa ya wuce iyakarsa da ya tsoma baki akan yadda iyayengidansa Kuraishawa za su zabi sarkinsu. Shi kuwa yana daukar kansa a matsayin wanda ya ke da fifiko akansu domin kuwa ya sami daukaka da matsayi ne daga Musulunci, saboda haka shi ne wanda ya fi dacewa ya tsoma baki akan yadda za a zabi halifan musulmi. Ba ya fahimtarsu, su ma ba su fahimtarsa. Kowane bangare yana kallon lamarin ne da mahangarsa ta kashin kansa. Kowane yana da ma’auni na shi na kanshi… Kusurwowi biyu ne da ba za su taba haduwa ba. Tasirin Azabtarwa Akan Halayyar Ammar. Tarihin rayuwar Ammar na musamman ne,wanda ya ke cike da izina ga wanda ya ke son daukar darasi. Za mu iya daukarsa a matsayin kyayyawan misali na mutumin da ya rayu a kaskance sannan ya yi gwagwarmaya mai tsawo ya hau matakalan kaiwa ga matsayin da ya kere na wadanda su ke yi masa kallon wulakanci. ( kuraishawa bangaren Umayyawa na jahliyya da kuma munafikansu da Musulunci ya ci su da yaki.) Wani abu da ya dace a yi ishara da shi anan shi ne cewa, a lokacin da Ammar ya musulunta ya fuskanci ukuba da azabtarwa daga Kuraishawa da wani mahaluki bai fuskanci irinta ba. Ammar ya shahara ne saboda azabtarwar da Kuraishawa su ka yi masa. Labarin yadda aka azabtar da shi, yana a matsayin kyakkyawan misali ne na irin tursasawar da Kuraishawa su ke yi wa mabiya sabon addini. Ammar, ya kebanta da cewa ana azabtar da shi shi da danginsa a lokaci guda. Wannan azabtarwar ce ta yi sanadiyyar mutuwar mahaifiyarsa da mahaifinsa. An kuma jefo da dan’uwansa daga kan katanga ya mutu akan tafarkin Musulunci. Tabon azabtarwa bai rabu da fatar jikin Ammar ba har zuwa karshen rayuwarsa. Muhammad Ibn Ka’ab al-Qardhy ya bada labarin cewa: “ Wata rana ya ga gadon bayan Ammar da ya ke a bude. Sai ya ga tabon rauni ajikinsa. Da ya tambaye shi sai Ammar ya fada masa cewa: Wannan alamun azabtarwar da Kuraishawa su ka rika yi mani ne akan rairayin Makka mai kuna.” ( Littafin Abdullah al-Subaiti da ya gabata.) Ga dukkan alamu, wannan mummunar azabtarwar ta haifar da kwantacciyar kiyayya ga Kuraishawa a cikin boyayyen hankalin Ammar. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne a wannan rayuwar ta duniya, a ce an azabtar da wani mutum irin azabar da aka gasawa Ammar, a kuma kashe mahaifinsa, da mahaifiyarsa da kuma dan’uwansa ta hanyar azabtarwa sannan kuma a ce ya mance.- Sai dai idan jaki ne ba mutum ba. Abu ne mai yiyuwa a ce wannan kwantacciyar kiyayyar ta yi tasiri a cikin halinsa. Watakila kuma tasirin hakan ya karu, a lokacin da ya ga mutanen da a baya suka azabtar da shi, an wayi gari sun sake samun aiko a lokacin Usman. Watakila a wannan lokacin ya tunano da mawuyacin halin da ya shiga a lokacin da aka kashe mahaifinsa da mahaifiyarsa da kuma dan’uwansa ta hanyar a zabtarwa akan rairayin Makka. Aduk lokacin da Ammar ya ga wani Bakuraishe mai jan wuya a gabansa yana saurin zaginsa. Su kuwa Kuraihsawa masu jan wuya suna shayinsa saboda matsayinsa a wurin annabi, sannan kuma da wurin Abubakar da Umar daga baya. Bisa karamin dalili Ammar yana zaginsu su kuwa su kyale shi. An ambaci cewa wani lokaci ya zagi Khalid Bin Walid, sai Khalid din ya je waurin annabi ya fada masa cewa: “ Ya manzon Allah ya kyale wannan bawan yana zagina? Wallahi ba domin kai ba da bai zage ni ba.” (Littafin da ya gabata na Abdullahi al-Subaiti) Wata rana kuma ya zagi Amru Bin As. Sai Amru ya maida masa jawabi na makirci a gaban mutane da cewa: “ Ka zage ni alhali ni ban zage ka ba.” Ya kuma zagi Abbas Ibn Abi Lahab a wani wuri. (al-Awasin Minal Qawasim: Ibn Arabi.) A lokacin shawarar zabar Usman, Ammar ya dauki matsayi mai tsanani. Baya son a zabi Usman, Ali Ibn Abi Talib ya ke so a zaba. Kai kace yana daukar Usman a matsayin mai wakiltar Kuraishawa. Lokacin da aka zabi Usman, Ammar ya ji zafi sosai ya mike a cikin masallaci yana fada. Ya kuma ci gaba da nunawa Usman adawa har zuwa karshe. (al-Fitnatul-Kubrah: Taha Hussain.) Tushen Halin Son Daidaito Da Adalci Na Ammar: Mun bayyana cewa Ammar Bin Yasir ya sha banban da Abu Zar a halayyarsa. Abu Zar balaraben kauye ne da ya fito daga cikin kabila. Shi kuwa Ammar dan birni ne daga cikin Makka kuma daga cikin ajin mutane raunana. Halayyar balaraben kauye ta banbanta da ta dan birni daga tushe. ( Introduction To Sociology: Dawson & Gettys.) Idan mu ka yi nazarin ginshikin halayyar Abu Zar, za mu fahimci cewa da akwai dabi’u na larabawan kauye a tare da ita. Ya saba da rayuwar daidaito a cikin kabila da kuma raba ganimar yaki daidai wa daidai a tsakanin ‘ya’yan kabila da kuma sauran albarkatu. Watakila wannan yana daga cikin dalilan da su ka sa Abu Zar ya ke yin kira da samar da daidaito ta fuskar dukiya a tsakanin mutane. Shi kuwa Ammar, yana yin kira ne zuwa ga wani abu na daban. Shi dan gwagwarmaya ne kamar Abu Zar, watakila ma ya fi Abu Zar tsanani a cikin gwagwarmayarsa da Kuraishawa. Sai dai shi baya yin kira zuwa ga samar da daidaito a cikin dukiya kamar yadda ya ke yin kira zuwa ga kyautata imani. Ya yi imani da cewa Kuraishawa kafirai ne wadanda su ke bayyana cewa su musulmi ne. Yana danganta musu kafirci kai tsaye. Wata rana ya bayyana haka: “Usman ya kafirta, bakin kafirci.” ( Littafin Ibn Arabi da ya gabata.) A lokacin da ake tsakiyar yakin Siffain wani mutum ya tambaye shi cewa: “Ya Aba Yaqzan.. Ashe manzon Allah ba ya fadi cewa, ku yaki mutane har sai sun musulunta ba. Idan su ka musulunta to suna da kariya ta jininsu da dukiyarsu.” Mai tambaya yana nufin Mu’awiyya da mutanensa. Sai Ammar ya fada masa cewa: “ Na’am haka ne… Sai dai su sun mika wuya ne amma suna boye da kafirci har zuwa lokacin da su ka yi karfi.” (al-Subaiti: Littafin da ya gabata.) Ammar ya yi imani da cewa Kuraishawa ba su musulunta da gaske ba, sun mika wuya ne saboda an fi karfinsu, su ka rika nuna Musulunci a zahiri domin samun dama. Ammar, ya fuskanci Amru Bin As lokacin yakin Siffain ya kuma tuhume shi da kafirci. Amru Bin As ya yi furuci da Kalmar shahada a gaban Ammar sai Ammar din ya ce: “ Yi shiru, ba ka aiki da ita tun a lokacin da annabi Muhammadu ya ke a raye da kuma bayan wafatinsa.” An rawaito cewa a lokacin yakin Siffain Ammar ya yi huduba wacce ta ke cike da karfin hali da kuma kalubale. Ya fadawa mutanen da ya ke a tare da su cewa: ”Ya ku bayin Allah! Ku yunkura a tare da ni mu fuskanci wadannan mutanen da su ke riya cewa suna neman daukar fansar jinin mutumin da ya zalunci kansa (Usman), wanda kuma ya dora kansa akan bayin Allah yana yi musu hukuncin da wani abu wanda Allah bai saukar da shi ba a cikin littafinsa. Wadanda su ka kashe shi bayin Allah ne salihai masu hani da wuce gona da iri wadanda kuma su ke yin umarni da kyautatawa. Sai wadannan mutanen- wadanda idan duniyarsu ta yi kyau basu damu ba idan addini ya gurbata- su ka fadi cewa, me ya sa ku ka kashe shi? Sai mu ka ba su jawabi da cewa: Saboda ya zo da sabon abu. Sai su ka ce bai zo da wani abu sabo ba. Sun fadi haka ne saboda ya basu abin duniya da su ke so amma suna sane da cewa shi azzalumi ne. Su mutane ne da su ka dandani zakin duniya su ka kuma kaunace ta sannan kuma su ka ji dadin mulkinta. Ku sani cewa idan ma’abocin gaskiya ya zama jagoransu to zai shiga tsakaninsu da abinda su ke morewa a cikinta. Su mutane ne da ba su da wani tarihi a Musulunci da za su cancanci a yi musu biyayya da kuma zama jagorori amma sun yaudari mutanensu da fadin cewa: An kashe jagoranmu bisa zalunci, saboda su fake da wannan domin su zama masu dagawa da mulki irin na ma’abota duniya. Wannan makirci ne da su ka kulla wanda kuma ya kai koli kamar yadda ku ke gani. Ba domin haka ba, babu wani mutum da zai yi musu mubaya’a. Ya Allah idan ka taimake mu to dama ka saba yin taimako. Idan kuma ka ba su nasara to ka yi musu tanadin azaba mai radadi saboda bidi’ar da su ka kirkiro a cikin bayinka.” (Littafin Abdullah al-Subaity wanda ya gabata.) Wanda ya ke kore cewa Ammar zai iya fadin wannan magana dangane da mabiya Mu’awiyya, ya mance da cewa Ammar din yana yaki da su da takobinsa kuma yana ganin halaccin zubar da jininsu. Abinda aka sani dangane da Ammar shi ne cewa yana daukar kiyayyar da Kuraishawa su ke yi wa Ali ne kamar yadda a baya su ka yi kiyaya da manzon Allah, ba tare da wani banbanci ba. A zahiri, Ammar ba ya iya yi wa kansa linzami akan hakan. Zuciyarsa tana cike da kin jinin kuraishawa ta yadda ba zai iya boyewa ba. Ba ya dagawa wani daga cikin kuraishawa hula idan ba Abubakar da Umar da kuma wani gungu na Banu Hashim ba. Ya yi imani cewa, Usman ya kaucewa tafarkin magabatansa. Boren da Ammar ya yi wa Kuraishawa yana kunshe da ban mamaki. Bai damu da musuluntar da su ka yi ba, ko kuma ibadun da su ke yi na zahiri. A wurinsa addini shi ne kyakkyawar mu’amala. Amma furta Kalmar shahada da kuma yin ibadu wasu abubuwa ne na zahiri da ba su wadatarwa. A wurin Ammar, addini shi ne shimfida daidaito a tsakanin bayi da iyayengijinsu a rabon mukami da matsayi. Yana kuma kin jinin jagorori masu girman kai yana kuma daukarsu a matsayin kafirai da su ke dodorido da addini. Kyautata Mu’amala, shi ne Musulunci a wurin Ammar ba shiga ta zahiri ba. An rawaito cewa wani mutum daga cikin sahabban Ali ya zo wurinsa (Ammar) a tsakiyar yakin Siffai yana yi masa kuka akan wani mafarki da ya yi wanda ya ke damunsa. Ya fada masa halin da ya samu kansa da cewa: “ Na fito daga cikin mutanena ina mai neman gaskiya wacce mu ke akanta kuma ba ni da shakku akan cewa wadancan mutanen (Mu’awiyya da rundunarsa) suna kan bata. Ban gushe akan haka ba sai wannan daren da mu ke ciki….. Sai wani mai kira ya gabata yana shaidawa da cewa babu wani abin bauta sai Allah kuma Muhammadu manzon Allah ne. Ya kuma yi kiran salla. Sai wani mutum daga ckinsu ya yi wannan irin kiran. Sai aka kabbara salla mu ka yi sallar jam’i tare. Kuma mu ka yi addu’a guda sannan mu ka karanta kur’ani guda, annabinmu kuma guda daya ne. Sai shakku ya shige ni a cikin wannan daren. Na wayi gari a cikin wani hali wanda babu wanda ya san shi sai Allah. (littafin Abdulhamid Sahhar wanda ya gabata.) Wannan mutumin yana cikin tsaka mai wuya. Yana ganin dukkan bangarorin biyu a matsayin wadanda su ke bin addini guda, suna kuma yin Kalmar shahada guda, da yin salla guda a tare da juna. Sai ya yi wa kansa tambaya to me ya sa su ke yaki da juna? Ya zo wurin Ali yana yi masa wannan tambayar. Sai Ali ya fada masa cewa ya je ya sami Ammar saboda ya yi masa bayani. Shi kuwa wannan mutumin ya je yana neman Ammar a tsakanin mutane yana kiran sunansa. Da ya same shi sai ya bashi labarin rudanin da ya fada ciki. Nan take sai Ammar ya bashi yankakken jawabi wanda babu shakku a cikinsa. Ammar ya fadi cewa: Tutocin da su ke fuskantarsa a wannan lokacin su ne dai wadancan tutocin da su ka fuskance shi a lokacin Badar da kuma Uhudu. Daga nan sai Ammar ya daga murya yana cewa: “Wallahi da ace za su yi ta kawo mana hari da takubbansu har su ka tura mu zuwa yabanyar Hajar ( wani wuri mai nisa daga inda su ke yaki) to da na kara samun yakini akan cewa ina kan gaskiya su kuma suna kan bata. Rantsuwa da Allah, babu yadda za a yi a sami zaman lafiya har sai daya daga cikin bangarorin biyu ya yi furuci da cewa suna kan kafirci, sannan kuma su yi furuci da cewa daya bangaren yana kan gaskiya…“ Ga dukkan alamu Ammar yana son ya ci gaba da yin yaki ne har ya tilastawa kuraishawa sun yi furuci da cewa suna kan bata ne. A zatona wannan ba abu ne mai yiyu wa ba. Wanda ya ke son cimma wata manufa babu yadda za a yi ya yi furuci da cewa yana kan bata. Ammar ya yi gwagwarmaya mai tsawo a tare da annabi har sai da kuraishawa su ka mika wuya ga wadannan manufofin da ya yi gwagwarmaya saboda su. Kuraishawa sun mika kai sau daya, ba kuwa za su sake mika kai ba a wani karon. Mai hankali ba a sarinsa sau biyu a cikin rami guda, mumini ne shi ko zindiki. Batu ne na dukiya da more jin dadin rayuwa da kuma ni’imomi. Babu yadda za yi wanda ya ke more jin dadin rayuwa ya rabu da jin dadinsa cikin sauki saboda wani ya bukace shi da ya yi hakan. (Yana Da Ci Gaba…) Mujtaba Adam ne ya fassara wannan makalar Ana iya samunsa ta wannan email din nigeria3000@yahoo
Posted on: Tue, 17 Sep 2013 23:22:04 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015