Assalamu alaikum.Da fatan kun wayi gari lafiya.Ku kasance da mu a - TopicsExpress



          

Assalamu alaikum.Da fatan kun wayi gari lafiya.Ku kasance da mu a shirye-shiryenmu na safe da hantsi domin jin halin da duniya ke ciki. A ciki za ku ji cewa yayin da kasashen duniya ke murnar shiga sabuwar shekarar 2014 a kalandar Gregory shugaban #Nigeria, Goodluck Jonathan, ya ce matakan da yake dauka na hana wawure dukiyar yan kasar sun sa ta tsira da sama da naira biliyon 120 a shekarar 2013. Kuna ganin haka ne? Shi kuwa shugaban Korea ta arewa, Kim Jong-un, ya ce kisan da aka yi wa bappansa ya kawo ci gaba a kasar. Masu sa ido sun ce nan gaba kadan za a fara tattaunawar zaman tsakanin shugaban #Sudan ta kudu da tsohon mataimakinsa, wanda ya yi tawaye. Ku biyo mu domin jin karin bayani.Mun gode
Posted on: Wed, 01 Jan 2014 04:21:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015