BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI DA MAZIYYI DA KUMA WADIYYI via: Hausa - TopicsExpress



          

BAMBANCI TSAKANIN MANIYYI DA MAZIYYI DA KUMA WADIYYI via: Hausa Bakwai7 via: 0- 1. Maniyyi Maniyyin namiji : ruwa ne mai kauri FARI wanda yake fitowa ya yin babbar shaawa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino, ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshin kwai. Maniyyin mace : ruwa ne tsinkakke, MAI FATSI-FATSI, WANI LOKACIN KUMA YANA ZUWA FARI, wanda yake fitowa ya yin babbar shaawa kamar saduwa, ko wasa da farji, sannan yana tunkudo juna lokacin da yake fitowa, sannan za ta ji tsananin shaawa da kuma dadi lokacin da ya fito, kuma warinsa yana kama da warin hudar dabino ko damammen gari, Idan ya bushe kuma yana yin kamshi kwai, kuma za ta ji shaawarta ta yanke bayan fitowarsa. HUKUNCINSA SHI NE : YANA WAJABTA WANKA 2. Maziyyi : Ruwa ne tsinkakke da yake fitowa, yayin karamar shaawa, kamar tunanin aure ko kuma tuna wacce kake so, ko matarka, ko kallon matar ko namijin da kike shaawa, haka nan yana fitowa yayin wasa tsakanin miji da mata, saidai shi ba ya sa shaawa ta tafi, kuma wani lokacin baa sanin ya fito. Malamai suna cewa : Maziyyi ya fi fitowa mata, fiye da maza, lokacin da maziyyi zai fitowa namiji azzakarinsa zai mike. HUKUNCINSA SHI NE A WANKE FARJI GABA DAYA, DA KUMA INDA YA SHAFA, KUMA A SAKE ALWALA 3. Wadiyyi wani ruwa ne mai kauri da yake fitowa a karshen fitsari, ko kuma karshen bahaya ga wanda ya jima bai yi ba, yana fitowa ga wadanda suke fama da gwauranci ko wadanda suka yi nisa da abokin rayuwarsu ta aure, ina nufin namiji ko mace. YANA DAUKAR DUKA HUKUNCE-HUKUNCEN FITSARI admin #D_Babson
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 20:57:56 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015