DAGA MAJLISIN TAFSIRAN SUNNAH. . Daga Gwallaga Juma‘at Mosque - TopicsExpress



          

DAGA MAJLISIN TAFSIRAN SUNNAH. . Daga Gwallaga Juma‘at Mosque Bauchi. Tare da Dr. Muh‘d Sani Umar R/Lemo . Ayau asabat 24-ramadan mal. Yaci-gaba da karatune daga aya ta 12 cikin suratul-isra‘i . Fadin Allah ta‘ala..... وجعلناالليل والنهارءايتين فمحونا ءاية الليل وجعلنا ءاية النهار مبصرة لتبتغو فضلا من ربكم...... . Ma‘ana Allah yace:- sai muka sanya dare da yini amatsayin ayoyi (abun rula) guda 2, sai muka 6oye ayan dare (ma‘ana muka 6oye haskenshi), sai kuma muka sanya ayan yini afadake, (munyi hakanne) don ku samu daman nema daga falalan ubangijinku, kuma don kusan adadin lissafin shekaru, da kuma kidayen kwanaki, Kuma komai (daka sani dama wanda baka sani ba) mun tsarashi ne tsarawa. . Mal. Saiyace gaba da lissafo/ciro FiQh da ayan take Qunshe dasu, yace da rana ne ake lissafin shekaru kamar yadda da watane ake lissafin kwanaki, kuma wata daga rana take samun haskenta, sannan mal. Ya bayyana wasu daga cikin amfani da kowanne ya ta‘allaQa dashi . Misali Amfanin da rana ta Qunsa 1-da rana ake neman abinci halal (galibi) 2-da rana ne akafi samun kuzari 3-da rana ne ake komai a fa‘dake 4-da rana ne tsirrai suke toho 5-da rana ne sauran halittu sukafi walawa, 6-rana ni‘ima ce tako wani fanni. . Afamin/ayyukan dare 1-an sanya dare ne don da zama lokacin hutu ga bawa 2-dare tufafine ga bayi 3-dare lokacin nutsuwan dukkan halittu ne 4-dare lokaci ne na samun nutsuwar kwakwalwa 5-dare ni‘imace tako wani sashi . Daga karshe mal. Ya karanto ayannan ta suratul-Qasas aya ta 71-72 . Allah yace:- kace dasu (ya muhammad) ya kuke gani inda ace Allah ya sanya muku dare tazarce harzuwa ranan tashin Qiyama, ko ya sanya muku rana tazarce har tashin Qiyama, wa kuke dashi wanda zai canja muku su suna sassa6awa ? . Amsa itace babu, . Allah ya saka wa mal. Da alkhairi. *snn01*
Posted on: Sat, 03 Aug 2013 18:49:06 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015