DON ALLAH KU BOYE SUNANA. Assalam! Ni matashi ne dan kimanin - TopicsExpress



          

DON ALLAH KU BOYE SUNANA. Assalam! Ni matashi ne dan kimanin shekaru 33, haifaffen garin kaduna, ina da mata dayaya, kuma ina aikine a babban birnin tarayya wato ABUJA. A ranar wata asabar da sassafe na tafi tasha don hawa motar kaduna, sai na tadda wata mace kyakkyawa a zaune a motar, kuma dama mutum daya ake jira motar ta cika, don haka daga hawana sai motar tatashi. Tashinmu keda wuya, sai na fara jan wannan mata da hira domin wallahi tayimin kwarai da gaske, na samu tirjiya amma daga baya sai ta bani hadin kai, mukayi ta hira da wasanni irin na masoya, a inda ta nuna min cewa, ita zama ta wuce kaduna, a zatona sai kawai na hukunta zaria zata, don haka da zan sauka sai na karbi lambarta kana nace mata bayan awa biyu (2Hours) zan kira inji ya kika sauka tace min to. Haka ko akayi domin bayan kimanin awa biyu sai na rangadawa wayarta kira, aka kuma dace ta shiga koda ta dauka sai tace min bata isa gida ba, amma idan ta karasa, zata yimin flashing. Can kusan faduwar rana kuwa sai ta kira tace minta sauka lafiyatun daga wannan lokaci muke yawan magana da ita a waya. Hakika mun shaqu kwarai sai dai duk lokacin dana zurfafa cikin kalmomin soyayya sai tace min ba nine mutum da ya fada mata hakan ba, amma hakan bai hana a gujeta ba, kuma wannan yasa na shiga cikin tsananin bukatar sanin labarin wannan yarinya, nayi tunanin ko tanada aljanu ne? Amma danayi mata wasu tambayoyi sai na gane aa bata dasu, koda na matsa da bincike sai na gano ashe GURGUWA ce! Shi yasa ake gudunta, gashi ta kamu da masifar sona, kuma nayi alkawarin bazan yaudare taba, kuma ni bazan iya auren gurguwaba, don haka na yanke shawar zuwa wannan shafi domin neman gudum mawar ku, don Allah yaya zanyi? Kuma wallahi ni dai ina sonta. Ga kuma alkawarin danayi mata. Gashi kuma ta bayyanam min gurguwace!!! Kuma ni bazan iya auren gurguwaba, menene shawararku,
Posted on: Mon, 04 Nov 2013 21:28:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015