DUNIYAR NAN WANDA BAI ZO BA MA TANA JIRANSA! Duk jaruntar mutum, - TopicsExpress



          

DUNIYAR NAN WANDA BAI ZO BA MA TANA JIRANSA! Duk jaruntar mutum, wata rana sai ta mayar da shi rago. Duk iliminka kuma, wata rana sai ta mayar da kai kamar jahili. Duk isarka, wata rana sai ta mayar da kai kasashshe. Abinda da yake baka tsoro, wata rana sai ya baka tausayi. Abinda ke baka haushi, wata rana sai ya baka dariya. Idan kana ganin ka fi kowa, wata rana zaka ga wanda ya fika. Idan kana ganin kowa ya fika, wata rana zaka ga wanda ya gaza ka. Wanda ke zaginka, wata rana zai wayi gari babu abin da zai zaga. Wanda kai kuma ka tsana, wata rana zaka wayi gari ya mutu balle kaji haushinsa. Wanda ka ki, wata rana shi zaka so, wanda kuma ka so wata rana shi zaka ki. Idan ka zalunci wani don kafi karfinsa, wata rana wani zai zalunceka don yafi karfinka. Idan ka tuno wani abu, sai ya saka kai kuka, wata rana kuma in ka tuno wani abu, sai kai dariya. Yanuwa mu dai yi fatan Allah yasa mu ci jarabawa kawai, domin duniya nan ta wuce tunanin mu. Hakika duniya itace gonar lahira, Allah yasa mu shuka alkhairi kuma mu girbi alkhairi ya kuma sa mu gama da duniya lfy!
Posted on: Tue, 22 Oct 2013 21:26:11 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015