Dandalin Abota, ko Dandalin Badakala? Babban abin da yafi ban - TopicsExpress



          

Dandalin Abota, ko Dandalin Badakala? Babban abin da yafi ban cikin alamuran matasanmu a dandalin facebook shi ne, rashin manufa takamaime a yayin da suke shawagi da shantakewa a dandalin. Abu na farko da aka sansu da shi shi ne yawan ruduwa da yan mata. Duk wacce ka shiga shafinta a dandalin facebook in dai budurwa ce, za ka ga kashi 90 cikin abokananta maza ne. Da zarar ta yi tari, ko mhmm ta rubuta a shafinta, nan take za ka ga taaliki (comments) daga maza sama da hamsin kafin saa guda. Duk abin da tace sai an ce wani abu a kai. balle ta loda hoto a shafin. Ba sai na gaya muku abin da zai faru ba. Su kansu yan matan haka suka fi so. Musamman wasu ke daukan hotuna su loda a shafinsu, don su ji me samari za su ce. Idan kana karanta sakonnin da matasa ke rubutawa dangane da wadannan hotuna sai ranka ya baci. Wai duk nan yabonta ake. Abu na biyu shi ne yaudara. Su kansu wasu daga cikin yan matan karya suke yi, hotunan wasu suke lodawa suce nasu ne. Su ma samarin suna haka. Don haka galibin samarinmu, ba duka ba, idan ka shiga shafukansu ba abin da za ka gani sai surutai kan yan mata, da wasannin kwallon kafa da hotunansu, da abubuwa marasa kima. Wanda hakan ke nuna cewa mai wannan shafin ya shigo ne kawai don yayi ta walagigi mara maana. Abu na gaba shi ne cin mutuncin abokin magana. Da yawa daga cikin matasa a dandalin facebook ba su da daa, musamman dai a majalisun da ake tattaunawa kan abubuwan da suka shafi alumma. A daya daga cikin manyan majalisun da ke shafin facebook na matasanmu, na sha karanta zage-zage, da surutan cin mutuncin abokin zance; ba kunya ba tsoro. A wasu lokuta sai na sa baki alamuran ke sassautawa. Wannan bai dace ba. Sai kuma batun batsa da ashararanci. Wannan kuma ya kasu kashi biyu. Akwai zantuka da wasu matasanmu ke yi kan hotunan yan mata da niyyar yabo, ko kokarin gamsar da yan matan cewa suna da kyau. Idan ka karanta ire-iren wadannan zantuka sai ranka ya baci. Sai kuma yaudara, wanda wannan ruwan dare ne a dandalin facebook. Da yawa cikin mutane kan rubuta abin da ba shi bane hakikanin rayuwarsu. Wannan tasa idan kana karanta bayaninsu a Profile sai ka ga akwai tufka da warwara. Misali, yarinya ko matashi zai ce musulmi ne shi, mai son Manzon Allah, mai kishin musulunci, littafinsa shi ne Kurani da Hadisi, amma idan aka zo wajen Hobbies ko Interests, watau abin da yake shaawa a rayuwarsa ko rayuwarta, sai ka ga ya zayyana sunayen manyan makiyan Allah daga cikin mawakan turai, da miyagun fina-finan da a zahiri suna cin mutuncin addini ne, ko ma wasunsu duka cike suke da batsa da rashin tarbiyya. Wannan tufka da warwara ne ko shakka babu. Galibin matasa idan ka shiga Profile dinsu za ka ta cin karo irin wannan. Abu na gaba shi ne yawan kankamba da fadi-ba a tambayeka ba. Akwai majalisa ta musamman da ake amsa tambayoyi kan alamuran addini, maana majalisa ce ta fatawa dai a takaice. Akwai wadanda aka killace musamman don amsa tambayoyi, wanda hakan ya kamata daman. Tun da shariar musulunci na gudanuwa ne cikin tsari, sannan ba kowa bane ke da kudurar amsa fatawa, domin amana ce. Amma abin mamaki da zarar wani ya aiko tambaya, kafin wadanda aka killace su bayar da amsa, nan take za ka mutum yayi caraf ya fara magana, a ciki yana cewa: …a gani na abu kaza hukuncinsa kaza ne. Ko …a fahimta ina ganin kaza zai zama kaza. Sai kace an nemi shawararsa. Ya mance cewa ilmi amana ce, kuma ba a gudanar alamuran addini da jahilci. A wannan majalisar har wa yau, da zarar mace ta aiko tambaya, kafin a bayar da amsa nan take samari sama da goma sun fara tofa albarkacin bakinsu, duk dai don neman samun shiga. Mun dauki addini abin wasa. Abu na gaba shi ne rashin sirri. Da yawa daga cikin matasa har yanzu sun kasa fahimtar mummunar hadarin da ke tattare da rashin sirri. Idan kana son fahimtar hakan kuwa sai ka shigo dandanlin facebook. Da wanda ke kwance a kan gado yana hutawa, da wanda ke cin tuwo miyar kuka, da wanda ke zance budurwarsa, da wanda ke shan shayi, da wanda ke kan hanyar tafiya zuwa wani garin, da wanda zai shiga wanka, da wanda ke sanya tufafi, duk za ka gani a facebook, matasanmu sun shigar. Ba ruwansu da mai zai je ya dawo. A sauran kasashen da suka ci gaba a fannin sadarwa, zantuka irin wadannan sun yi sanadiyyar mutuwar wasu, da hasaran rayuka, da taaddanci, da rasa matsayin siyasa da shugabanci, da karyewar arziki, da mutuwar auratayya da dai sauransu. To amma matasanmu ko a jikinsu, wai an tsikari kakkausa. Kari a kan haka har da hotuna marasa kan gado. Wasu hotunan ma basu kamata a ce an nuna su ga duniya ba, amma a shafin facebook duk za ka gansu. Abu na gaba shi ne kankamba wajen latse-latse da matse-matse. A kaidar yadda shafin facebook ke gudanuwa, duk halin da abokanka ke ciki ana sanar da kai ne. Idan abokananka suka kalli wani hoto ko bidiyo da Intanet ta hanyar manhajar facebook, za a sanar da kai. Matsalar ita ce, da zarar an sanar da kai, sai kaji kaima kana son ka kalla, da zarar ka matsa shikenan, hoton ko bidiyon ba zai bude ba, sai an kaika asalin shafin. Ba wannan bane matsalar, galibin ire- iren wadannan hotuna da bidiyo na batsa ne, amma kai ba za gani a fili, da zarar ka matsa, nan take za a kai wa abokanka sanarwa cewa ka kalli hoto ko bidiyo kaza, mai dauke da batsar, amma kai ba za ka gani ba. Ka ga a nan kai baka ga wannan hoto ba, amma an kai wa abokanka sanarwa cewa ka gani. Idan mai mutunci ne kai, kimarka ta zube kenan a idonsu. Matasanmu duk basu lura da wannan. Duk abin da muka ga ana yi sai kawai mu ma muyi, ko bamu san amfaninsa ba. Wadannan kadan ne cikin badakalar da ke faruwa a dandalin facebook kan abin da ya danganci matasanmu.
Posted on: Sat, 09 Nov 2013 12:12:50 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015