Dandalin ban dariya Wasu manyan yan siyasane sundawo daga - TopicsExpress



          

Dandalin ban dariya Wasu manyan yan siyasane sundawo daga zabe suna tafiya a mota sai sukai hadari a saitin gonar wani bafillace motar ta hantsile tai alkafira duk suka sume shikuma dan fulani yana zaune yaga abinda yafaru sai ya tafi yakai agaji dayaje duk yagansu a sume sai yaitunanin kosun mutu sai ya haka rami agun yamirgino wani kato acikinsu yadda a raminnan yarufe yakara haka wani yazo zai kara sa wani sai wani acikinsu yamotsa dakyar yace kai bamutuwa mukai ba shiko gogannaka ko sauraronsa beyiba yamirgino shima yaddana shi aramin duk saida yahaka rami yasakasu yaje yasamu guri yazauna domin yahuta zamansa keda wuya yaji jiniyar yan sanda suka zo sukatambayeshi dan Allah bakaga wasu yan siyasa da sukai hadari ananba sai dan fillo to nidai naga sunyi hadari duk barai nahaka rami nabinnesu amma naji wani a cikinsu yana cewa ba mutuwa mukaiba to yallabai kasan yan siyasa da karya suna iya mutuwa suce basu mutuba
Posted on: Sat, 22 Jun 2013 06:23:26 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015