Duk wanda ya kalli Zanga-zanga farkonta da karshenta, amma da idon - TopicsExpress



          

Duk wanda ya kalli Zanga-zanga farkonta da karshenta, amma da idon shariah da ingantaccen madubin hankali, zai tabbatar da cewa, BA ABIN DA YAKE CIKINta face sharri; makaryaci ne ko shi wanene; wanda yace, akwai ta lumana da sabaninta. Alhali babu lumana cikin saba wa Allah da manzonsa, da karkacewa ga barin tafarkin magabata na kwarai. Babu lumana a cikin cike wa mutane hanyoyinsu, Babu lumana cikin bata wa mutane katangun su da fenti, Babu lumana cikin muggan maganganu ga shugabanni. ALLAH maida mabarnata turba ta gyara.
Posted on: Mon, 21 Oct 2013 10:54:23 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015