El-Maude Ahmad > wrote!!! ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA YA - TopicsExpress



          

El-Maude Ahmad > wrote!!! ASH-SHEIKH ALBANI ZARIA YA GARGADI JAMAATU AHLUSSUNNAN NIGERIA. =ooo=oo=oo==ooo ==oo==ooo==oo=o oo= Mashahurin malamin addinin musuluncin nan dake jagorancin Daruul-Hadeethi s-Salafiyyah dake masarautar Zazzau, Ash-Sheikh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, yayi kira ga daukacin ahlussunnan Nigeria dasu zamo tsintsiya madaurinki daya, kuma su dunkule irin dunkulewar nan da babu wani sauran rabuwa har abada. Wannan kira ya fito ne Adaidai lokacin da bangarori biyu na izalatul bidia waiqamatussunn ah suke kokarin fashewa. Sheikh Albani ya ce, a halin da musulmin kasar nan suke ciki a yau, babu sauran nasarori daza a samu indai kungiyar izala ta fashe. Ya ce dacin haduwa ya fi zakin rabuwa sannan duk inda aka ce haduwa cikin alheri ne toh ta fi rabuwa akan alheri, ballantana rabuwa kan sharri da kiyayya. Saboda haka, Ya yan uwana Ahlussunnah ina kiranku domin girman Allah ku yayyafa ma zukatanku ruwa. Ku hadu wuri guda ku yi yafiya tsakaninku, kudawo da kaunar juna da girmama juna. Sannan kuma ku yi taka tsantsan da yan siyasa da sarakunan gargajiya da shehunnan bidia da suke da gaba da kiyayya kan wannan kungiya. Ash-Sheikh Albani Zaria ya kara da cewa; Ahlussunnah ku dawo cikin hayyacinku domin duk wani dan bidia a halin yanzu ya sa6a bindiganshi akan kune kuma babu wani nasara daza ku samu akan shi indai kuna wargaje. Malamin daga karshe ya ce, wannan babbar masifa ce, ana ji ana gani wasu kalilan daga jamaa wadanda basu wuce mutum biyar zuwa goma ba suna kokarin wargaza miliyoyin ahlussunnah. Sai ya kara da cewa Allah ba zai kyale wannan lamari ba haka face yayi hukunci muddin ba a yi gyara ba.
Posted on: Thu, 07 Nov 2013 20:58:39 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015