FILIN: ALKALI SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAHU) TARE DA - TopicsExpress



          

FILIN: ALKALI SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI (RAHIMAHULLAHU) TARE DA LITTAFIN: AL-AKIDATUSSAHIHAT, BI MUWAFAKATUS SHARI’A NA SHAYKH ABUBAKAR MAHMUD GUMI WANDA YA FASSARA: ALHAJI INUWA BABA (MFR) Almajirin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi FCT. Abuja Nigeria. MAI RUBUTU: UMMU ABDILLAH ZARIA HANYA INGANTACCIYA DA TA DACE DA SHARI’AH ///03 MUQADDIMAR MALAM (2) Kuma Annabi mai tsira da aminci ya ce, “Rayuwata alkhairi ce a gare ku, kuma mutawa ta ma alkhairi ce a gare ku.” (Abin nufi a nan shi ne, rayuwarsa alkhairi ce saboda shiryarwa da alkhairi da ake samu a wajensa, haka ma mutuwarsa alkhairi ce, saboda hukune-hukunce ya tsaya ke nan a kanmu). Allah Shi ne masani a kan haka. To, wannan Ya nuna cewa ba wani abin da zai zobayan mutuwarsa, in kuma wani ya ce ga wani abin ya zo to, ya yi shishshigi ken an a addini. Don ba wani abu da zai sake zuwa na sako, don kuwa Allah Ya nuna cewa shi ne karshen manzo da zai zo ba wani ke nan. Saboda Allah Ya ce: «Annabi ba mahaifin daya daga cikin ku ba ne sai dai shi manzon Allah ne kuma cikamakin Annabawa. Allah Ya kasance masani ne a kan komai » [Ahza : 40]. Kuma Annabi mai tsira da aminci ya ce, “Misalina da Annabawa da wadanda suka gabace ni, kamar misalin katanga ce da aka gina ta ta yi kyau ta ba da kayatarwa sai tubalidaya ya rage, a cika katangar inda kowa ya zoya gani sai yace, ina ma wannan tubalin a cikashi don ta cika kawata ?” Sai Annabi ya ce: “Nine wanda aka cike wannna wuri na tabalin daya da ya rage” Sai ya ambata cewa, “Ni ne wannan tubalin, da ni aka cika wannan tubalin ba wani Annabi bayana.” [Bukhari da Muslim ne suka ruwaito]. Annabi mai tsira da aminci ya ce, “Ni ne mai share duhu, kuma da ni ne Allah yake share kafirci, kuma ni ne wanda za a tara mutane a gabana, ni ne kuma karshen Annabawa wanda ba wani Annabi a bayana.” [Bukhari da Muslim]. Annabi mai tsira da aminci ya ce : “A cikin jama’ata za a sami makaryata guda 30, kowanne yana cewa shi Annabi ne, to kada ku yarda da su. Karya suke yi. Ba wani Annabi bayana.” [Abu Dauda da Ahmad da wasunsu]. Kuma an sami Hadisi daga Imam Muslim cewaAnnabi mai tsira da aminci ya ce: “An fifita ni a kan Annabawa da abubuwa shida: (1) An ba ni matattar magana. (2) An ba ni ikon duk inda zan je yaki sai an jarrabe su da tsoro, (3) An halarta mini cin ganima. (4) An sa mini kasa ta zama masallaci kuma wuri mai tsarki. (5) Kuma an aiko ni ga dukkan talikai baki daya. (6) Ni ne kuma cikamakin Annabawa, bawani Annabi bayana.” [Imam Tirmizi kuma ya ce Hadisin ingantacce ne]. In sha Allah zamu ji cigaba a cikin littafin “AL-AKIDATUSSAHIHAT, BI MUWAKATUS SHARI’AH” na Alqadiy Shaykh Abubakar Mahmud Gumi, Allah Ya yi masa rahama.
Posted on: Sun, 25 Aug 2013 09:42:41 +0000

Trending Topics



ght:30px;">
Loving Sai ram brothers and sisters! It was 6 years ago on 31
I have witnessed this ceremony in person and it is one of the most
HALLOWEEN O.. VISPERA DE TODOS LOS
This is why Obama is in office, because Paul Ryan was the other

Recently Viewed Topics




© 2015