Hakika saurin fushi yana daga cikin mugayen dabiu wadanda - TopicsExpress



          

Hakika saurin fushi yana daga cikin mugayen dabiu wadanda musulunci yake nuna mana mu gujesu. Wani mutum yazo yace wa Manzon Allah (saww): YA RASULALLAHI (ina son) KAYI MIN WASIYYA Shi azatonsa Annabi (saww) zai zaunar dashi yace masa yi kaza kabar kaza ko yai masa wasu jawabai masu tsawo. Amma da yake MANZON NAMU (saww) Allah ya azurtashi da JAWAMIUL KALIMI (wato kalmomi yan kadan masu tattarowa maanoni da yawa). Sai yace masa: KAR KAYI FUSHI (Sahihin hadisi ne yazo ta hanyoyi fiye da biyar ingantattu) Me yasa Annabi (saww) yace masa kar yayi fushi? Sai malamai sukace saboda fushi yana daga cikin MANYAN KOFOFIN DA SHAYTAN YAKE SHIGOWA TA CIKINSU DOMIN YA HALLAKAR DA BIL ADAMA. Fushi mummunar Dabia ne wadanda akullum yake jefa maabotansa acikin Baqin ciki da nadama da hasara da gaaba da yan uwa, da yanke zumunci da kiyayya da munana zato. Sau da yawa mukan gani idan shaidanun aljanu sunyi sunyi sun kasa shiga jikin bil adama, sukan koma gefe ne su jirashi sai lokacin da yake cikin fushi sannan su samu nasarar shiga jikinsa. Fushi yana kore mutum daga samun yardar Ubangiji. Fushi yana hana mutum samun nutsuwa a zuciyarsa. Kuma yana hana mutum aikata alkhairi. Don haka a yawaita karatun Alqurani da sauraronsa ko yaushe. Insha Allahu zaa rika jin sanyi a zuciya. Sannan a rika yawaita bibbiyar tarihin magabata na kwarai domin daukar darasi a harkokin rayuwa. A rika karanta wannan adduar ta Annabi Musa (as) RABBISH RAH LEE SADREE WA YASSIR LEE AMREE Insha Allahu zaa samu saukin zama da kowa. A rika karanta wannan adduar: ALLAHUMMAJ ALNEE SABIRATAN WAJALNEE SHAAKIRAH Da kuma adduar Nana Aisha (rta) ALLAHUMMA INNAKA AFUWWUN KAREEMUN TUHIBBUL AFWA FAAFU ANNEE Ya Allah ka gyara mana zukatanmu mu zama masu biyayya agareka ko yaushe. Ameen.
Posted on: Tue, 15 Oct 2013 06:30:42 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015