IDAN YAN ALJANNAH SUN SHIGA ALJANNAH, kuma suka ga cewa basu ga - TopicsExpress



          

IDAN YAN ALJANNAH SUN SHIGA ALJANNAH, kuma suka ga cewa basu ga wasu daga cikin abokansu na nan duniya ba, Zasu tambayi Ubangiji game dasu. Zasu ce: Ya Ubangiji! Ina abokanmu, masoyanmu su wane da wane? Mun kasance muna yin sallah da Azumi tare dasu aduniya. Yaya bamu gansu anan ba?. Nan take sai Ubangiji ya umurci Malaikunsa suje cikin wuta su zaga su fitar da duk wanda yake da imani azuciyarsa koda misalin kwayar zarrah ne.. Imam Hasanul Basary (rah) yace: Ka yawaita abokanai mutanen kirki aduniya. Domin zasuyi ceto agareka rananr Alkiyamah. Cikakken aboki shine wanda zai yi maka dalilin shiga aljannah in ya samu dama. Ibnul Qayyim Aljauziyyah yana kuka yana gaya ma Almajiransa cewa : Don Allah idan baku ganni atare daku agidan Aljannah ba, ku tambaya game dani. Kuce Ya Ubangiji akwai wani bawanka wanda ya kasance yana tunasar damu game dakai â¦â¦â¦ (sai ya sake fashewa da kuka). ALLAHU AKBAR!! â Da wannan nake rokon alfarma wajenku bayin Allah Nagari, masoyan Allah da Manzonsa (saw). DON GIRMAN ALLAH ku tuna dani idan har baku ganni ba.. Kuce ya Allah akwai wani bawanka mai rauni, Maabocin So da Qaunar AnnabinKa (saw).... Please don Allah kar ku manta dani... (Tearsí ½í¸­í ½í¸­í ½í¸­). Please share dis with your contacts including me so that all Muslim brothers and sisters would remember you.
Posted on: Sun, 12 Oct 2014 20:46:52 +0000

Trending Topics



Recently Viewed Topics




© 2015